Farashin Mai Ya Ɗan Sauko a Wasu Jihohi bayan Matakin Matatar Dangote

Farashin Mai Ya Ɗan Sauko a Wasu Jihohi bayan Matakin Matatar Dangote

  • Wasu gidajen mai sun rage farashin litar fetur zuwa ƙasa da bayan matakin matatar Dangote ta dauka ya kawo sauƙi
  • Matatar Dangote ta sauke farashin fetur daga N1,275 zuwa N1,250 kan kowace lita a farashin tanka da ake dauko wa
  • Masana sun danganta raguwar farashin da saukar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya bayan rikicin Amurka da Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos–Wasu gidajen sayar da mai da ke kan titin Legas zuwa Ibadan da kuma wasu sassan jihohin Legas da Ogun sun rage farashin fetur zuwa ƙasa da N1,300 kan kowace lita.

Wannan na zuwa ne bayan da Matatar Mai ta Dangote ta sanar da rage farashin fetur da dizal a ƙarshen makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Dattawan Kwara sun yi barazana da 2027 bayan kashe masu mutum 1200 a mulkin Tinubu

An samu ragin farashin litar fetur
Alhaji Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote Hoto: Bloomberg/Contributor
Source: Getty Images

Jaridar Punch ta tattaro cewa matakin ya nuna ƙudirin matatar na samar da man fetur mai sauƙin samu ga 'yan Najeriya tare da taimakawa harkokin tattalin arziki a faɗin ƙasar.

Matatar Dangote ta rage farashi

Premium Times ta wallafa cewa Dangote ya rage farashin fetur daga N1,275 zuwa N1,250 kan kowace lita a farashin tanka, yayin da aka rage farashin dizal daga N1,800 zuwa N1,700 kan kowace lita.

A ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2026 an lura cewa wasu gidajen mai na MRS da ke yankin Mowe/Ibafo a jihar Ogun sun daidaita farashin fetur zuwa N1,286 kan kowace lita.

Haka kuma, gidajen mai na NIPCO da Heyden sun sayar da fetur kan N1,290 a kowace lita, yayin da SGR ke sayarwa kan N1,297.

Sai dai har yanzu gidajen mai da dama na ci gaba da sayar da fetur sama da N1,300 kan kowace lita duk da saukin da takwarorinsu suka yi.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta gyara zargin da ake yi wa Tukur Mamu kan hada kai da Boko Haram

Dalilin saukin farashi fetur a Najeriya

Matatar Dangote ta ce sake duba farashin wani ɓangare ne na ƙoƙarin ta na ƙara inganta samar da mai a cikin gida da kuma rage wa masu amfani da mai kashe kuɗi.

Matatar Dangote ta yi ragin mai bayan farashi ya sauko a kasuwar duniya
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote yana jawabi a wajen wani taro Hoto: Bloomberg/Contributor
Source: Getty Images

Kamfanin ya bayyana cewa hakan zai taimaka wa harkokin sufuri, samar da wutar lantarki da masana'antu waɗanda ke amfani da kayayyakin man fetur sosai wajen gudanar da ayyukansu.

An kuma lura cewa gidajen mai da dama sun rage farashin dizal zuwa kusan N1,800 kan kowace lita daga N1,900 da aka saba sayarwa a baya.

Tun bayan fara aiki, matatar Dangote mai ƙarfin tace ganga 650,000 a rana ta ƙara samar da kayayyakin man fetur ga kasuwar cikin gida domin rage dogaron Najeriya ga shigo da mai daga ƙasashen waje.

Dangote ya kara farashin mai

A wani labarin, kun ji cewa matatar Dangote ta sanar da karin kudin mai ga manyan diloli da ke sayen kaya a wajenta bayan shiga 2026 yayin da ake ci gaba da rikici kan mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Amurka ta ware N5bn don ba da kwangilar bibiyar cin zarafin addini a Najeriya

Rikici a kan mashigar ya jefa kasuwar man duniya a cikin wani hali, lamarin da ya jawo tashi da saukar farashin man fetur a kasuwar duniya, musamman a lokutan da sabanin ke kamari.

Rahotanni sun nuna cewa tun bayan karin farashin da matatar Dangote ta yi, yawancin gidajen mai sun kara kudi, amma ’yan kasuwa sun lura da raguwar sayen mai, inda aka ce mutane na rage yawan amfani da fetur .

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng