An Shiga Tashin Hankali a Katsina da 'Yan Bindiga Suka Sace Wasu Ɗaliban Jami'a

An Shiga Tashin Hankali a Katsina da 'Yan Bindiga Suka Sace Wasu Ɗaliban Jami'a

  • ‘Yan bindiga sun sace daliban jami’ar FUDMA a Katsina, bayan farmaki da suka kai Graveyard Quarters da misalin karfe 2:40 na dare
  • Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun kai dauki don hana ‘yan bindigar tserewa, amma maharan sun riga sun bar yankin kafin su iso
  • A Adamawa, jami'an tsaro sun ceto Babawuro Abdullahi, wanda aka yi garkuwa da shi, a Jigawa an kama malami bisa kashe almajiri

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - ‘Yan bindiga sun sace dalibai biyu na jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) a jihar Katsina, bayan kai farmaki da safiyar Talata.

Maharan sun afka unguwar Graveyard Quarters da ke kan titin Tsaskiya a garin Dutsin-Ma da misalin karfe 2:40 na dare, inda suka sace daliban.

Rundunar 'yan sanda ta cafke masu laifi a Adamawa da Jigawa yayin da 'yan bindiga suka sace dalibai a Katsina
Rundunar 'yan sanda ta cafke masu laifi a Adamawa da Jigawa yayin da 'yan bindiga suka sace dalibai a Katsina. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun sace daliban jami'ar FUDMA

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun gwabza kazamin fada da ƴan bindiga, an kashe mutum 1 a Katsina

Wasu majiyoyi sun tabbatar da an sace daliban, amma har yanzu ba a bayyana cikakken bayansu ba, a cewar rahoton Zagazola Makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce:

"Bayan samun kiran gaggawa, jami’an tsaro sun kai daukin gaggawa don hana ‘yan bindigan guduwa tare da kokarin ceto wadanda aka sace."

To sai dai kuma, bayanai sun nuna cewa jami'an ba su samu nasara nan take ba, domin maharan sun tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Rahoton ya ce majiyoyin tsaro sun ba da tabbacin cewa ana ci gaba da aikin bincike da kokarin ganin an kubutar da daliban da aka sace.

An ceto wani da aka sace a Adamawa

Ana haka ne kuma aka samu labarin cewa ‘yan sanda Adamawa tare da hadin gwiwar mafarauta sun ceto wani mutumi mai shekaru 60, Babawuro Abdullahi, daga hannun masu garkuwa.

An ceto shi ne a yankin Dikir Hill da ke Dumne, karamar hukumar Song, bayan da aka kai farmaki kan maboyar masu garkuwan.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa yan ta'adda bazata, sun hallaka rikakken ɗan bindiga a Zamfara

Rahotanni sun nuna cewa bayan musayar wuta mai zafi, an kubutar da wanda aka sace bayan shafe kwanaki 17 a hannun ‘yan bindigar.

Jami’an tsaro sun kwato bindiga guda ɗaya a bayan harin, yayin da wadanda ake zargi suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Babu wani jami’in tsaro da ya rasa ransa a yayin farmakin, kuma ana ci gaba da bincike don kamo masu laifin da suka tsere.

An kama malami bisa kashe almajiri a Jigawa

'Yan sanda sun kama malamin da ya kashe wani almajiri a Jigawa
Malamin da aka kama a Jigawa bisa zargin kashe almajiri ya amsa laifinsa a gaban 'yan sanda. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

A wani labari, ‘yan sanda a Jigawa sun cafke wani malamin tsangaya, Mallam Musa Wada, bisa zargin kashe wani almajiri, Bashir Adamu, dan shekara 14.

An tsinci gawar yaron a yankin Jikas-Dabaja, da ke karamar hukumar Gwaram, tare da yankakken kai da wasu sassan jikinsa.

Rahotanni sun ce an gano gawar a ranar 12 ga watan Maris, 2025, inda bincike ya kai ga kama Malllam Musa Wada mai shekaru 35.

Kara karanta wannan

'Yan fashi sun kai hari makaranta ana suhur a Katsina, sun yi kisan kai

A lokacin bincike, wanda ake zargi ya amsa laifinsa, ya kuma nuna wa jami’an 'yan sanda da ke binciken lamarin inda ya binne sassan jikin almajirin.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargi da zarar an kammala bincike.

An kama mata da harsasai a hanyar Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar 'yan sanda ta samu nasarar cafke wata mata mai suna Hauwa Sani da harsasai 124 za ta kai wa 'yan bindiga a Katsina.

An kama Hauwa Sani dauke da harsasai 124 da aka ɓoye a cikin galan din manja mai lita biyar, kuma ta amsa cewa wani Nasiru daga Daura ne ya ba ta domin ta kai Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng