Gwamna Ya Fadi Bangaren da Buhari Zai Yi Wa APC Amfani a Zaɓen 2027

Gwamna Ya Fadi Bangaren da Buhari Zai Yi Wa APC Amfani a Zaɓen 2027

  • Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana muhimmancin Muhammadu Buhari a APC tare da kuri’unsa miliyan 12 a 2027
  • Sule ya ce tsohon shugaban na da matukar tasiri ga nasarar APC, kuma hadin gwiwarsa da Tinubu na kara karfi
  • Gwamna ya gode wa Bola Tinubu bisa goyon baya da karin kudin da sauran alheri da yake bai wa jihar Nasarawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi magana kan tasirin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Gwamna Sule ya bayyana cewa har yanzu Buhari babban ginshiki ne ga jam’iyyar APC a zaben 2027.

Gwamna ya fadi tasirin Buhari a zaɓe
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana muhimmancin Buhari a ga APC a zaɓe. Hoto: Gov. Abdullahi Sule.
Asali: Twitter

Gwamna ya tuna kuri'un Buhari miliyan 12

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron maraba da Sakataren Gwamnatin Jiha, Barista Labaran Magaji a fadar gwamnati da ke Lafia, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sule ya ce kuri’un Buhari har miliyan 12 za su sauya lissafi domin amfani da jam’iyyar mai mulki a zabe mai zuwa.

Sule ya soki masu tunanin cewa Buhari da magoya bayansa za su fice daga hadakar da ta haifi APC, yana mai cewa Buhari har yanzu jagora ne.

Ya kara da cewa Buhari da Shugaba Bola Tinubu sun shafe lokaci tare, sun kuma taka rawar gani wajen kafa APC, Punch ta ruwaito.

Gwamnan Nasarawa ya yi magana kan magajinsa

Game da zaben Nasarawa, gwamnan ya amince cewa za a samu hadin gwiwa da samun daidaito a tsakanin masu neman kujerar gwamna a jihar.

Ya tabbatar da cewa mutane 20 sun nuna sha’awarsu ta tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben 2027.

Sai dai ya ce Allah ne kadai ke bayar da mukami ga wanda yake so a lokacin da yake so.

Ya ce:

“Abin da nake gani kenan, za a samu hadin gwiwa da aiki tare, domin daga karshe mutum daya ne zai ci.

“Allah ne zai zabi sabon gwamnanmu ba A.A. Sule ba. Don haka mu marawa wanda zai zama gwamna a 2027 baya."
Gwamna ya fadi muhimmancin Buhari ga APC
Gwamna Abdullahi Sule ya ce Buhari yana da tasiri ga jam'iyyar APC. Hoto: Gov. Abdullahi Sule Mandate, Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Gwamna Sule ya yi godiya ga Bola Tinubu

Gwamna Sule ya gode wa Shugaba Tinubu bisa goyon baya da karin kudi da sauran alheri da yake bai wa Nasarawa da sauran jihohi.

Ya ce saboda karamcin shugaban kasa, Nasarawa na iya biyan albashin wata uku ba tare da kudin tarayya ba.

Ya kara da cewa:

“Ba don nuna isa ba, sai dai saboda yadda muke sarrafa kudin jiharmu, domin haka duk rana ta 25 muna biyan albashi a jihar Nasarawa."

Gwamna ya musanta cewa Buhari zai bar APC

Kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa cewa Buhari, da tsofaffin ministocinsa ƴan tsagin CPC na shirin barin APC.

Gwamna Sule ya ce tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Abubakar Malami da sauran tsofaffin ƴaƴan APC na nan daram a jam'iyya.

Game da zaben 2027 da ke tafe, gwamnan ya yi magana kan masu neman takara inda ya ce dole masu nema su marawa mutum ɗaya baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.