Hukumar EFCC Za Ta Binciki Ministan Tinubu da Ake Zargin Ya 'Wawure' Sama da N500bn
- Wata ƙungiyar matasan APC (APC-YLA) ta gudanar da zanga-zanga kan batun binciken ministan tsaro, Bello Matawalle
- Matasan sun buƙaci EFCC ta sake buɗe binciken Matawalle kan zargin da ake masa na sama da faɗi da dukiyar Zamfara lokacin da yake gwamna
- EFCC ta karɓi bukatar masu zanga-zangar, inda ta tabbatar masu cewa za ta ci gaban da binciken tsohon gwamnan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta bayyana cewa za ta binciki zargin karkatar da dukiyar al'umma da ake yi wa Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle.
Hukumar EFCC ta sha alwashin cewa za ta kakkaɓe takardun Matawalle, ta ci gaba da bincike dangane da zargin wawure Naira biliyan 528 da ake masa lokacin yana gwamnan jihar Zamfara.

Asali: Facebook
EFCC ta ci gaba da binciken ministan Tinubu
Wannan tabbaci ya fito ne ranar Juma’a yayin wata zanga-zanga da ƙungiyar matasan jam’iyyar APC (APC-YLA) ta gudanar a hedikwatar EFCC da ke Abuja, Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagoran ƙungiyar, Mohammed Ireji, ya buƙaci EFCC da ta ci gaba da bincike kan zargin da aka gabatar tun da daɗewa.
Ireji ya ya jaddada cewa an riga an shigar da ƙorafe-ƙorafe tun a watan Mayu da Satumba 2024, amma babu wani ci gaba da aka gani.
Zargin almundahanar da ake yi wa Matawalle
Zarge-zargen almundahanar da aka gabatar gaban EFCC kan Matawalle sun haɗa da:
- Naira biliyan 290 daga rabon FAAC
- Naira biliyan 133 daga rabon JAAC
- Bashin Naira biliyan 105 da ba a san yadda aka kashe su ba
Da yake karɓar takardar ƙorafi, Daraktan Tsaro na EFCC, Idowu Adedeji, ya ce: “Mun karɓi ƙorafinku kuma za mu mika shi wurin da ya kamata.”
Masu zanga-zangar sun tuna yadda EFCC ta samu nasarori wajen binciken da ta gudanar da gurfanar manyan mutane irin su Betta Edu, Yahaya Bello, da Darius Ishaku.

Asali: Twitter
Me yasa matasan suka yi zanga-zanga?
Bisa haka matasan suka nemi hukumar EFCC ta gaggauta ɗaukar mataki kan zarge-zargen almundahana da talauta lalitar gwamnatin Zamfara da ake yi wa Matawalle.
A rahoton Punch, jagoran masu zanga-zangar ya ce:
"Mun zo nan ne domin mu jawo hankalin EFCC ta sake buɗe fayil ɗin binciken ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle wanda ta rufe.
"Muna da bayanai da hujjojin da ke tabbatar da cewa tsohon gwamnan ya yi rub da ciki da dukiyar talakawan Zamfara."
Matawalle ya tarewa Tinubu faɗa a Arewa
A wani labarin, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya soki wasu ƴan siyasar Arewa da ke sukar Bola Tiɓubu.
Matawalle ya yi ikirarin cewa galibin masu fitowa suna sukar mai girma shugaban ƙasa, suna haka ne domin neman suna.
Ya kumaa ƙaryata ikirarin da ke cewa Tinubu barazana ne ga siyasar Arewa, yana mai cewa irin waɗannan maganganu ba su da tushe balle makama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng