Ba Jira: Ministan Tsaro, Matawalle Ya Fadi Shirin Sojoji kan Dokar Ta Baci a Rivers

Ba Jira: Ministan Tsaro, Matawalle Ya Fadi Shirin Sojoji kan Dokar Ta Baci a Rivers

  • Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle ya goyi bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan sanya dokar ta ɓaci a Rivers
  • Matawalle ya bayyana cewa matakin ya zama wajibi duba da yadda rikicin jihar ke kawo tangarɗa ga harkokin mulkin dimokuraɗiyya
  • Ministan ya nuna cewa sojoji suna cikin shirin ko-ta-kwana domin kare muhimman kayayyakin gwamnati daga barazanar tsageru

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana kan dokar ta ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya sanya a jihar Rivers.

Bello Matawalle wanda aka nada tun a 2023 ya bayyana cewa sanya dokar ta ɓacin a jihar Rivers, abu ne wanda ya zama wajibi.

Matawalle ya goyi bayan dokar ta baci a Rivers
Matawalle ya nuna goyon baya kan sa dokar ta baci a Rivers Hoto: Bello Matawalle
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama'a na ma'aikatar tsaro, Iyogun Sunday, ya fitar a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Rivers: Abin da manyan lauyoyi ke cewa kan matakin Tinubu na sa dokar ta baci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Bello Matawalle ya ce kan shirin sojoji?

Bello Matawalle ya bayyana cewa sojojin Najeriya na cikin shirin ko-ta-kwana don kare kayan gwamnati da tabbatar da tsaron mazauna jihar.

Ministan ya nuna goyon bayansa ga shugaban ƙasa kan wannan mataki, yana mai cewa hakan yana da matuƙar muhimmanci don dawo da kwanciyar hankali sakamakon rikicin siyasar jihar, rahoton The Cable ya tabbatar.

Ya bayyana cewa dokar ta-ɓaci mataki ne na dole domin magance rikicin siyasa da ke ci gaba da kawo tangarɗa wajen gudanar da mulkin dimokuraɗiyya da walwalar al’ummar jihar Rivers.

Yayin da yake yin bitar jawabin shugaban ƙasa game da dokar ta-ɓacin, ministan ya nuna cewa akwai buƙatar ɗaukar matakin gaggawa domin magance rikicin siyasar jihar.

"Duba da abubuwan da suke faruwa, ministan ya jaddada cewa sojojin Najeriya na cikin shirin ko-ta-kwana don kare gine-ginen gwamnati da tabbatar da tsaron ƴan ƙasa."
“Ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na kai hari ga wuraren gwamnati ko tayar da zaune tsaye zai fuskanci martani mai ƙarfi daga jami’an tsaro."

Kara karanta wannan

An gano inda Gwamna Fubara yake bayan sojoji sun mamaye fadar gwamnatin Ribas

- Iyogun Sunday

Matawalle ya damu da barazanar tsaro a Rivers

Matawalle ya nuna damuwa kan rahotannin shirin kai hare-haren da tsageru ke yi, yana mai jaddada buƙatar haɗin kai don dawo da zaman lafiya da tsaro.

Ya sake nanata cewa gwamnatin tarayya na da niyyar tabbatar da tsaron dukkan ƴan ƙasa da kare muhimman kayayyakin gwamnati a jihar Rivers.

Matawalle ya ƙara da cewa ma’aikatar tsaro da rundunar soji za su ci gaba da kare tsaron ƙasa tare da tabbatar da komawar jihar Rivers kan turbar zaman lafiya, kwanciyar hankali da mulkin dimokuraɗiyya.

Lauyoyi sun magantu kan dokar ta ɓaci a Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu manyan lauyoyi sun yi tsokaci kan matakin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na sanya dokar ta ɓaci a jihar Rivers.

Manyan lauyoyin sun bayyana cewa matakin da shugaban ƙasan ya ɗauka cike yake da kura-kurai masu tarin yawa.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Manyan zunubai 3 da Tinubu ya nuna Gwamna Fubara ya aikata

Sun nuna cewa shugaba Tinubu ya nuna son kai wajen dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da sauran zaɓaɓɓun jami'an gwamnatin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng