'Zuwansa Banza': Ƴan Kano kan Jita Jitar Zuwan Kwankwaso APC, Sun Yabawa Gawuna
- Kungiyar matasa da daliban APC a Kano ta ce komawar Rabiu Musa Kwankwaso ba za ta amfani jam’iyyar ba, saboda rashin tasirinsa yanzu
- KASASCO ta bayyana cewa NNPP na fuskantar rugujewa a Kano, inda yawancin jiga-jigan jam’iyyar suka koma APC tun bayan zaben 2023
- Matasan sun ce APC mai hamayya ta riga ta warware rikice-rikicen cikin gida, kuma za ta samu kuri’u sama da miliyan biyu a 2027 a Kano
- Sun gode wa shugabannin jam’iyya kamar Abdullahi Ganduje, Barau Jibrin da Nasiru Gawuna bisa rawar da suke takawa wajen karfafa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Kungiyar 'All Progressives Congress Youth and Students Council' a Kano ta yi magana kan siyasar jihar Kano da Najeriya.
Kungiyar matasan ɗaliban APC ta bayyana adawa da jita-jitar shirin dawowar Sanata Rabi’u Kwankwaso jam’iyyar APC.

Asali: Twitter
'Kwankwaso bai da amfani' - Matasan APC
Shugaban kungiyar, Yahaya Kabo ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka gudanar a Kano, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta ce dawowar Rabiu Kwankwaso ba za ta amfani APC ba ko ta ina, kasancewar tasirinsa a siyasa ya ja baya sosai yanzu.
Kabo ya ce:
“Jam’iyyar APC a Kano karkashin Hon. Abdullahi Abbas na da karfi sosai, tana da sanatoci biyu, ‘yan Majalisar Tarayya da na jiha.
“Daga cikin wadanda suka sauya sheka akwai Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdurrahman Kawu Sumaila, wanda ba za a ci zabe ba da su ba.
“Kwankwaso ya rasa tasiri a siyasa, yanzu yana neman mafaka ta siyasa, amma APC ba mafaka ba ce ga irin mutanen da ke kawo rikici.”

Asali: Facebook
Kwankwaso: Matsalolin da NNPP ke fuskanta
Kabo ya bayyana cewa NNPP na fuskantar matsaloli da watsewar jiga-jigan da suka taimaka mata ta lashe zabe a shekarar 2023 a Kano.
KASASCO ta ce APC ta daidaita rikice-rikicenta kuma tana maida hankali kan abinda ke gabanta, yayin da NNPP ke fuskantar rugujewa a Kano.
Ta bayyana cewa APC za ta samu kuri’u sama da miliyan biyu a Kano a zaben 2027 don Bola Tinubu da duk ‘yan takarar jam’iyyar APC, Tribune ta ruwaito.
“KASASCO ta yaba wa Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bisa kokarinsa da jajircewarsa wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar."
- Cewar Kabo
Kungiyar ta kuma yaba wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, bisa dabarunsa da suka sa 80% na 'yan Kwankwasiyya suka koma APC.
Sannan ta yabawa tasirin Injiniya Abubakar Kabir Bichi, ministoci, Nasiru Gawuna, Murtala Garo, Ado Doguwa, AA Zaura, Rabi’u Bichi da sauran jagororin jam’iyyar.
An buƙaci Kwankwaso ya hade da Tinubu
A wani labarin, kungiyar matasan Yarabawa ta roki Rabiu Musa Kwankwaso da ya watsar da kiran shiga hadaka domin jawo wa Bola Tinubu matsala.
Shugaban kungiyar, Hammer Olalekan, ya bayyana cewa hadakar da ake kokarin kafa wa ba ta da karfin da za ta iya kada APC.
Matasan kungiyar sun yi ikirarin cewa ko Kwankwaso bai shiga APC ba, Bola Tinubu zai sake lashe zabe a 2027.
Asali: Legit.ng