Rio 2016: Nigeria ta kwabsa a gabannin wasanta da Japan
A wani abin da ba za a iya mantawa da shi ba a tarihin gasar kwallon kafan Najeriya da Japan a gasar guje-guje da tsalle-tsalle na Olympics da ake yi a Rio ta kasar Brazil, shi ne yadda aka kwabsa wa ‘yan wasan kasa da shekaru 23 na kasar a filin wasa na Manaus

‘Yan wasan kwallon Najeriya da aka yiwa lakabi da Dream team VI sun duburburce a lokacin da aka saka wani take na daban a matsayin taken Najeriya a lokacin da ‘yan wasan suka fito cikin filin wasan domin rerewa.
‘Yan wasan kwallon Najeriyar sun yi sarororo a lokacin da ake sa taken da suka ayyana na Najeriya ne, amma ba hakan ba ne, a cewar rahotanni, ba a kuma canza taken zuwa na Najeriyar ba, tsawon wani ani lokacin da aka gano cewa an yi kuskure, ya Allah ko ganin yadda ‘yan wasan suka duburburce.
KU KARANTA: Dan wasan Super Eagles, Mikel Obi yayi sabon suna
Bayan soma wasan da kimanin minti biyu ne aka nemi gafarar jama’a na kuskuren da aka yi na rashin sanya taken da ya dace, wanda hakan ba zai rasa nasaba da rashin shirin kasar yadda ya kamata ba a gasar kwallon, a cewar wasu masu bibiyan lamarin.
Yan wasan na Najeriya sun iso Manaus ne inda za su kara da Japan, kimanin sa’oi biyar kafin soma wasan, bayan da suka makale a Atlanta ta Amurka, wannan bai hana ‘yan wasan yiwa Japanawa ruwan balabalai a inda aka tashi 5 da 4.
Asali: Legit.ng