Bankin Duniya: Najeriya Ta Karbi Rancen Dala Miliyan 215 domin Rabawa Talakawa

Bankin Duniya: Najeriya Ta Karbi Rancen Dala Miliyan 215 domin Rabawa Talakawa

  • Bincike ya nuna cewa bankin duniya ya ƙara sakin Dala miliyan 215 domin shirin bayar da tallafin kuɗi ga 'yan Najeriya
  • Jimillar kuɗin da aka riga aka saki yanzu ya kai Dala miliyan 530 daga cikin Dala miliyan 800 da aka amince da su a baya
  • Bayanai sun nuna cewa ana biyan gidaje miliyan 15 tallafin N25,000 na wata-wata tsawon wata uku karkashin sabon tsarin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta sake samun ƙarin rancen Dala miliyan 215 daga Bankin Duniya domin ci gaba da aiwatar da shirin tallafin rage raɗaɗin cire tallafin mai.

Wannan ya ɗaga jimillar kuɗin da Bankin ya fitar zuwa Dala miliyan 530 daga cikin Dala miliyan 800 da aka amince da su a matsayin rancen tallafi.

Bola Tinubu
Gwamnatin Najeriya ta samu karin rancen bankin duniya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Binciken da jaridar Punch ta yi a ranar Alhamis ya nuna cewa bankin duniya ya kara sakin kudi zuwa asusun Najeriya kwanan nan, duk da cewa ba a bayyana ranar da aka tura su ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na nuni da cewa an saki kuɗin ne a baya-bayan nan kuma watakila cikin watan Mayun 2025 aka tura su.

Bankin Duniya ya amince da wannan rance tun a ranar 16 ga Disamba, 2021, domin bayar da tallafin kuɗi ga gidajen talakawa a Najeriya.

Sabon tsarin biyan tallafi a gidaje

A da, tsarin tallafin ya tanadi N5,000 ne ga kowane gida da aka tantance, amma an samu sauyi bayan zuwan Bola Tinubu.

Sababbin sauye-sauyen manufofi da gwamnatin Bola Tinubu ta kawo sun canza tsarin zuwa N25,000 na wata-wata tsawon wata uku da ya shafi gidaje miliyan 15 a fadin ƙasar nan.

A watan Oktoba da Nuwamba na 2023, Bankin Duniya ya saki sama da Dala miliyan 300, wanda ya kai jimillar kuɗin da aka saki zuwa Dala miliyan 315 a wancan lokacin.

Tinubu
Ana sa ran cigaba da biyan kudin tallafi bayan samun rancen bankin duniya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Sai dai sabon bayani da aka samu a ranar Alhamis ya tabbatar da cewa Bankin ya ƙara sakin Dala miliyan 215, wanda hakan ya kai jimillar zuwa Dala miliyan 530.

Wannan ya nuna cewa tuni Najeriya ta karɓi kusan 66.25% na jimillar kuɗin rancen, inda 33.75% kacal ya rage a cikin Dala miliyan 800 da aka amince da su tun farko.

Jinkirin aiwatar da shirin ya jawo asara

Ko da yake an amince da wannan rance tun 2021, aiwatar da shirin ya samu jinkiri har na tsawon watanni 17 kafin a fara sakin kuɗin.

Duk da wannan jinkiri, Najeriya ta ci gaba da biya wa Bankin Duniya bashin ruwa na rance da ya zarce Dala miliyan 6.18 kafin fara amfani da kudin.

Rahotannin Bankin Duniya sun tabbatar da cewa an riga an biya wasu kudin ruwa a watan Janairu da kuma Yuli na 2024 karkashin yarjejeniyar IDA-70190.

Majalisa ta nemi bayani kan kudin kwangila

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta nuna fargaba kan gaza biyan wasu makudan kudin 'yan kwangila.

A karkashin haka majalisar ta gayyaci manyan jami'an gwamnatin tarayya su gurfana a gabanta domin bayani game da kudin.

Majalisar ta bayyana cewa rashin biyan kudin yana kara jefa rayuwar 'yan kasa cikin wahala musamman mutanen karkara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng