Meta: Nigeria da Kasashe 5 da Suka Ci Tarar Kamfanin Facebook a Duniya

Meta: Nigeria da Kasashe 5 da Suka Ci Tarar Kamfanin Facebook a Duniya

Najeriya ta yi martani bayan kamfanin Meta da ya mallaki Facebook ya yi barazanar ficewa daga kasar saboda cin tarar shi duk da an masa irin hukuncin a kasashe da dama.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A makon da ya wuce kamfanin Meta da ya mallaki Facebook, WhatsApp da Intagram ya yi barazanar ficewa daga Najeriya saboda cin tarar shi.

Gwamnatin Najeriya ta ce hankalinta bai tashi ba saboda barazanar kamfanin, kuma ta lissafa kasashen da suka ci tarar Meta ba tare da ya musu wata barazana ba.

Facebook
Najeriya da wasu kasashen da aka ci tarar Facebook. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin kasashen da suka ci tarar meta saboda karya wasu dokokin mu'amala da ya yi bayan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Kasashen tarayyar Turai sun ci tarar Meta

Hukumar Kasashen Tarayyar Turai (EU) ta ci kamfanin Meta tarar da ta kai Yuro miliyan 797.72 saboda karya dokokinta.

Hukumar ta ce Meta ya tilasta wa masu amfani da Facebook aiki da sabis na talla a Facebook, tare da tauye 'yancin wasu kamfanonin talla.

A cewar hukumar, an fara binciken ne a shekarar 2021 kuma an tura wa Meta takardar zarge-zarge a 2022, wanda ya amsa a 2023.

Turai
Tarayyar Turai ta ci tarar Meta kan saba wasu dokoki. Hoto: Getty Images
Asali: Facebook

EU ta wallafa a shafinta cewa ta yanke hukuncin ne bayan cikakken nazari kan yadda Meta ke gudanar da harkoki a Turai.

An kayyade tarar Yuro miliyan 797.72 da aka ci Meta ne bisa tsarin da hukumar ta fitar a 2006, wanda ya duba tsawon lokacin da laifin ya ɗauka da kuma irin illar da ya janyo.

2. India ta ci tarar Meta kan saba doka

Hukumar CCI ta kasar India ta ci kamfanin Meta tarar dala miliyan 25.4 bisa sabawa ka’idar huldar kasuwanci.

Hakan ya biyo bayan binciken da aka fara tun a watan Maris na 2021 dangane da sabuwar dokar sirri ta WhatsApp.

Sabuwar dokar sirrin da WhatsApp ta gabatar a 2021 ta bayar da damar raba bayanan masu amfani da manhajar da sauran kamfanonin Meta, ciki har da Facebook da Instagram.

India
An ci tarar Meta a India. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Reuters ta wallafa cewa hukuncin ya janyo ce-ce-ku-ce a duniya baki daya, inda ake kallon hakan a matsayin keta 'yancin sirri.

Bayan cin tarar, CCI ta ce WhatsApp ba zai sake amfani da bayanan mutane don amfanin sauran manhajojin Meta ba sai dai domin gudanar da ayyukan WhatsApp kawai.

3. An shigar da Meta kara a Faransa

Tashar France 24 ta rahoto cewa Meta na fuskantar wata shari’a a Faransa bayan wasu manyan kamfanonin jarida sun kai shi kara bisa zargin karya dokokin kare bayanai.

Kamfanonin da suka hada da TF1, France Télévisions, BFM TV, Le Figaro, L'Express da Radio France ne suka shigar da karar.

Sun ce Meta na amfani da hanyoyi marasa dacewa wajen mallakar bayanan mutane da amfani da su domin tallace-tallace da ke hana sauran kamfanoni damar shiga gasa yadda ya kamata.

Maceon
Kamfanoni sun shigar da Meta kara a Faransa. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Duk da cewa ba a ayyana tarar da za a ci Meta a Faransa ba, ana hasashen za a iya cin kamfanin tara mai yawa.

4. Koriya ta Kudu ta ci tarar Meta

Hukumar kare bayanan sirri ta kasar Koriya ta Kudu ta ci kamfanin Meta tarar kusan Dala miliyan 15.67.

An ci tarar Meta a Koriya ta Kudu ne bisa zargin tattara bayanan masu amfani da Facebook ba tare da izini ba sannan ta mika su ga masu tallace-tallace.

Koriya
An ci tarar Meta a Koriya ta kudu saboda karya dokoki. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Reuters ta rahoto cewa hukunci na zuwa ne bayan wani bincike mai zurfi da hukumar ta gudanar dangane da ayyukan Meta a kasar.

5. An ci tarar Meta a Australia

Rahoton Tech in Asia ya nuna cewa kamfanin Meta ya amince da biyan Dala miliyan 50 kan karar dokokin sirri da aka shigar da shi a gaban kotu a Australia.

An zargi kamfanin da bari wani mai kirkirar manhaja na waje ya samu bayanan masu amfani da Facebook sama da 300,000 a kasar ba tare da yardarsu ba.

Australia
Australia ya ce tarar Meta saboda fitar da bayanai ba bisa sakaci da bayanan sirri. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Lamarin ya shafi yadda bayanan suka yi yawo har suka fada hannun wasu da suka yi amfani da su wajen tallata manufofin siyasa.

Meta ya gyara Facebook bayan samun matsala

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin Meta ya yi gyara bayan daukewar Facebook a dukkan sassan duniya.

An ruwaito cewa hatta wasu muhimman na'urorin kamfanin da suke babban ofishinsa sun samu tangarda a lokacin.

Sai dai tun daga lokacin faruwar matsalar kamfanin Meta ya sanar da cewa yana kan gyara kuma ya samu nasarar shawo kan kalubalen.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng