Yadda wata budurwa ta yi garkuwa da kanta domin samun kuɗi daga iyayenta

Yadda wata budurwa ta yi garkuwa da kanta domin samun kuɗi daga iyayenta

- Jami'an ƴan sanda a jihar Ekiti sun kama wata budurwa, Mary Idris da ta kitsa yin garkuwa da kanta

- Mary ta fadawa ƴan sanda cewa ta aikata hakan ne domin ta samu kudi daga hannun iyayenta domin ba su kula da ita

- An kama Mary Idris da wani Victor Olawuse da suka hadi baki a garin Akure na jihar Ondo bayan ƴan sanda sun bi didigin sakon da suka aike wa ƙanwar Mary

Ƴan sandan jihar Ekiti sun gabatar da wata mata mai suna Mary Idris da ta haɗa baki da wani ya yi garkuwa da ita domin karbar kuɗin fansa daga hannun iyayenta a ranar 9 ga watan Agustan 2020.

An kama Mary tare da wanda ta haɗa baki da shi, Victor Olawuse a Akure Jihar Ondo bayan ƙanwar ta ta samu saƙo cewa an sace yayan kuma a biya kuɗin fansa.

Yadda wata budurwa ta yi garkuwa da kanta domin samun kuɗi daga iyayenta
Yadda wata budurwa ta yi garkuwa da kanta domin samun kuɗi daga iyayenta. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kwanel Assimi Goita ya naɗa kansa shugaban ƙasa na mulkin soja a Mali

Kwamishinan ƴan sandan jihar Ekiiti, Tunde Mobayo wanda ya samu wakilcin Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Sunday Abutu yayin gabatar da wacce ake zargin yace;

"Mahaifiyar Mary ta zo ofishin mu ta yi rahoton cewa ƴar ta Mary Idris ta bar gida a ranar 9 ga watan Agusta misalin ƙarfe 4 na yamma tun ranar ba ta dawo ba.

"Ta ce anyi kokarin tuntubar ta a waya amma hakan ya ci tura. Bayan ɗan wani lokaci sai aka yi wa ƴar uwar ta sakon tes aka ce an yi garkuwa da Mary kuma aka nemi a biya kuɗin fansa.

"Rundunar ƴan sanda sun bi didigin lambar da aka aiko sakon tes ɗin da shi suka gano daga Akure, jihar Ondo aka turo saƙon inda aka tafi aka kamo Mary da wanda ta haɗa baki da shi, Victor Olawuse."

Mary ta amsa aikata laifin kuma ta ce ta aikata hakan ne domin ta samu kudi daga hannun iyayenta domin ba su kulawa da ita.

Ta ce;

"Na shirya sace kai na ne domin in samu kudi daga hannun iyaye na domin ba su kulawa da ni."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel