Garkuwa da mutane: Mai Ciki Tayi Karya, Miji Ya Biya Kudin Fansa, Ta Raba da Saurayinta

Garkuwa da mutane: Mai Ciki Tayi Karya, Miji Ya Biya Kudin Fansa, Ta Raba da Saurayinta

  • Yan sanda sun yi nasarar kama wata matar aure da saurayinta kan zargin yin garkuwa da kanta a birnin tarayya Abuja
  • Ana zargin matar mai suna Rosemary Ubah tayi garkuwa da kanta inda ta bukaci N2m daga mijinta wanda kuma tuni ya biya
  • Daga bisani rundunar 'yan sanda ta yi nasarar cafke Rosemary da saurayinta Walter inda suka tabbatar da aikata laifin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar 'yan sanda a birnin Abuja ta cafke matar aure da ta hada baki da saurayinta domin yin garkuwa da kanta.

Matar mai suna Rosemary Ubah wanda ke dauke da juna biyu ta aikata laifin ne tare da wani da ake kira Walter Ezeala.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan mutumin da ya sace Alkur'anai a Masallaci, ta ba shi zaɓi 1 a Abuja

Yan sanda sun yi nasarar kama matar aure da ta yi garkuwa da kanta
An kama matar aure a Abuja kan zargin garkuwa da kanta. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Yadda 'yan sanda suka samu rahotan

Rundunar 'yan sanda a birnin Abuja ta bayyana haka ne a jiya Litinin 20 ga watan Maris a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne a Saburi II Dei-Dei da ke birnin Abuja yayin da mijinta, Chiedozie Uba ya kai kara ofishin 'yan sanda da ke Gwa gwa.

Ubah ya fadawa rundunar cewa matarsa ta tafi da niyyar ganin likita sai aka kira shi kan cewa an yi garkuwa da ita.

Ya ce masu garkuwa sun bukaci N2m kudin fansa inda shi kuma bai yi wata-wata ba ya tura musu kudin nan take ta asusun bankin matarsa.

Bayan sakin matar, mijin ya dauke ta zuwa ofishin 'yan sanda inda a nan ne bayan fara bincike ta tabbatar da cewa hada baki suka yi da Walter.

Kara karanta wannan

A madadin yi wa budurwa 'Ramadan Basket', matashi ya sa mahaifiyarsa kukan daɗi

An cafke Walter kan zargin hadin baki

Daga bisani an kama Walter inda ya tabbatar da aikata laifin tare da karbar N800,000 a matsayin ladansa, ita kuma ta dauki N1,200,000.

Yayin da aka zurfafa bincike, an samu katunan cire kudi na bankin FCMB guda biyu da kudi N793,500 a hannunsu.

Rundunar ta tabbatar da cewa za ta tura su zuwa kotu da zarar ta kammala bincike a kansu.

Yan sanda sun yi korafi kan Murja

Kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun yi korafi kan 'yar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya kan kokarin bata musu suna a jihar.

Rundunar ta bukaci diyyar N500,000 daga hannun Murja inda ta ke zargin jarumar ta maka su a kotu ba tare da aikata wani laifi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel