Asiri Ya Tonu: An Kama Wata Budurwa da Ta Yi Garkuwa da Kanta da Wasu Mutane Sama da 50 a Jihar PDP

Asiri Ya Tonu: An Kama Wata Budurwa da Ta Yi Garkuwa da Kanta da Wasu Mutane Sama da 50 a Jihar PDP

  • Rundunar ƴan sanda ta kama wata mata da ta yi garkuwa da kanta tare da haɗin bakin saurayinta a jihar Akwa Ibom
  • Bayan ta shiga hannu, matar ta tabbatar da cewa ta haɗa baki da saurayinta da wasu mutum 3 domin su karbi kuɗi daga yayarta da ke kasar waje
  • Dakarun ƴan sandan sun kama wasu mutane 52 da zargin aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da kisa, garkuwa, fashi, asiri da damfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Akwa Ibom - ‘Yan sanda a Akwa Ibom sun ceto mutane hudu da aka yi garkuwa da su a cikin wata daya da ya gabata, ɗaya daga cikinsu ita ce matar da ta sace kanta.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, dakarun ƴan sandan sun kuma kama wasu mutane 52 bisa zargin aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar Akwa Ibom.

Yan sanda sun samu nasarori a Akwa Ibom.
Matar da ta yi garkuwa da kanta ta shiga hannu Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Kwamishinan rundunar ƴan sandan jihar, Waheed Ayilara, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Uyo ranar Jumu'a, 15 ga watan Maris, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce dakarun ƴan sanda sun kama mutum 52 bisa zargin aikata laifuka da suka haɗa da kisan kai, garkuwa da mutane, fashi da makami, safarar yara, asiri, da damfara.

Yadda wata mata ta yi garkuwa da kanta

CP ya ƙara da cewa daya daga cikin wadanda suka ceto ita ce wata mata daga kauyen Nung Oku a karamar hukumar Ibesikpo Asutan ta Akwa Ibom, wacce ta kitsa garkuwa da kanta.

Bayan ta gama dukkan wani ƙulli sai ta nemi a biya fansar Naira miliyan 4 amma daga bisani ƴan sanda suka damƙe ta.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar alƙur'ani sun turo saƙo mara daɗi

“Mun samu rahoto a ranar Litinin daga wata mai suna, Enobong Sampson cewa an yi garkuwa da ‘yar uwarta kuma masu garkuwa da mutane suna neman N4m a matsayin kudin fansa.
"Washe garin ranar Talata, ƴan sanda suka kama wacce ake zargin tare da saurayinta a wata maboya da ke Mbierebe Obio, karamar hukumar Ibesikpo Asutan.
"Ta amsa laifin cewa ta hada baki da saurayinta da wasu mutane uku domin sanar da cewa an sace ta don ta karɓi kudi daga hannun auntynta da ke zaune a kasar waje."

- CP Waheed Ayilara.

Kwamishinan ‘yan sandan ya tabbatar da cewa hukumar ƴan sanda zata gurfanar da dukkan waɗanda ake zargin da zarar an kammala bincike, Tribune Online ta rahoto.

Sheikh Gumi ya sa baki kan sace ɗaliban Kaduna

A wani rahoton kuma Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya yi magana kan ɗaliban da ƴan bindiga suka yi awon gaba da su a jihar Kaduna.

Malamin addinin musuluncin ya yi nuni da cewa amfani da ƙarfin tuwo kan ƴan bindigan ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel