Hukumar EFFC Ta Cafke Gudaji Kazaure kan Zargin Karbar Miliyoyi wajen Emefiele

Hukumar EFFC Ta Cafke Gudaji Kazaure kan Zargin Karbar Miliyoyi wajen Emefiele

  • Hukumar EFCC ta cafke tsohon ɗan majalisar wakilai, Gudaji Kazaure, bisa zargin karɓar Naira miliyan 70 daga hannun tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele
  • An kama Kazaure ne a ranar Laraba jim kaɗan bayan kotu ta cire umarnin da ya hana hukuma ɗaukar mataki a kansa, kamar yadda majiyar EFCC ta tabbatar
  • Majiyoyi sun ce cikin kuɗin akwai N20m da aka ba shi don sayen ragunan Sallah da kuma N50m a matsayin taimako bayan gobara ta auku a gidansa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta cafke tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kazaure a Jigawa, Hon. Muhammad Gudaji Kazaure.

Rahotanni sun bayyana cewa ana tunanin an cafke Gudaji Kazaure ne bisa zargin karɓar kuɗi daga tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Kazaure
EFCC ta cafke Gudaji Kazaure kan zargin badakalar kudi. Hoto: Gudaji Kazaure|EFCC|Central Bank of Nigeria
Asali: Facebook

Majiyar jaridar Daily Nigerian ta ce jami’an EFCC sun kama Kazaure ne a Kano a ranar Laraba, bayan wata babbar kotu a jihar ta janye umarnin hana cafke shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken hukumar ya nuna cewa Kazaure ya karɓi fiye da Naira miliyan 70 daga Emefiele a lokuta biyu.

Rahoto ya nuna cewa Gudaji Kazaure ya karbi kudin sayen raguna da gudunmuwa da aka ce an ba shi bayan gobara ta auku a gidansa.

Nawa Gudaji Kazaure ya karba wajen Emefiele?

Wata majiya daga hukumar EFCC ta bayyana cewa Kazaure ya karɓi Naira miliyan 20 daga wani wakilin Emefiele mai suna Mista Eric, a matsayin kuɗin sayen ragunan Sallah.

Bayan wannan kuma, an bayyana cewa Kazaure ya sake karɓar Naira miliyan 50 daga Emefiele a matsayin “tallafi” bayan da gobara ta kama gidansa.

RFI ta wallafa cewa majiyar ta ce EFCC ta kama shi ne domin amsa tambayoyi kan dalilin karɓar kudin.

Emefiele
An zargi Gudaji Kazaure da karbar kudi wajen Emefiele. Hoto: Central Bank of Nigeria
Asali: Facebook

A halin yanzu, an tsare Kazaure a ofishin EFCC da ke Kano, inda ake sa ran za a mayar da shi Abuja domin ci gaba da bincike da kuma gurfanarwa a kotu.

Tsohuwar matsayar Gudaji kan zargin Emefiele

A watan Disamba 2022, Kazaure ya zargi Emefiele da almundahana, yana mai cewa akwai bashin haraji har Naira Tiriliyan 89.1 da aka ce an ɓatar.

Ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamiti da shi ne shugaban sa domin bincikar wannan lamarin, amma aka hana shi damar gabatar da rahoton farko ga gwamnati.

Sai dai fadar shugaban kasa a wancan lokaci, ta bakin Garba Shehu, ta musanta zargin Kazaure, tana mai cewa ba gaskiya ba ne, kuma tuni aka rushe wannan kwamitin.

Rahotanni na nuna cewa kamun Hon. Kazaure yana daga cikin matakan da EFCC ke ɗauka wajen binciko hanyoyin da Emefiele ya bi wajen rarraba kuɗi ba bisa ƙa’ida ba a lokacin mulkinsa.

Godwin Emefiele a idon 'yan Najeriya

Ba Gudaji Kazaure kaɗai ba ne ya rika sukar Godwin Emefiele—tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).

A lokacin da yake kan kujerar mulki, musamman daga shekarar 2022 zuwa 2023, yawancin 'yan siyasa, masana tattalin arziki da masu sharhi sun nuna damuwa kan yadda ya tafiyar da manufofin kudi da kuma zarge-zargen almundahana da suka dabaibaye ofishinsa.

Ɗaya daga cikin fitattun batutuwan da suka janyo masa suka shi ne tsarin sauya takardun Naira da aka fara a ƙarshen mulkin Buhari.

Wannan mataki ya jawo wahala ga talakawa, ya tada tsadar rayuwa, kuma an ce an yi shi ne da manufa ta siyasa wajen takura wa wasu ‘yan takara.

Bugu da ƙari, akwai zarge-zargen batar da kuɗaɗe da suka shafi daruruwan biliyoyin Naira, da cin hanci wajen rarraba kudi ga kamfanoni da gwamnatoci.

Bayan ficewarsa daga ofis, gwamnatin Tinubu ta dakatar da shi, sannan EFCC da DSS suka kama shi bisa tuhumar almundahana, saba ka’ida wajen rarraba kudaden gwamnati, da kuma mallakar kadarori fiye da na albashinsa.

Har yanzu, bincike da gurfanarwarsa na ci gaba, lamarin da ke nuna cewa ba karamin jan hankali Emefiele ya jawo ba a tarihin shugabannin CBN.

Gaskiya kan rade radin kama Mele Kyari

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban EFCC da Bola Tinubu ya sauke, Mele Kyari ya ce ba a kama shi ba.

An yada maganganu a kafafen sada zumunta cewa an kama Mele Kyari sakamakon zargin badakala a kamfanin NNPCL.

Sai dai ya karyata hakan yana mai cewa a shirye yake ya yi bayani filla filla kan yadda ya shafe shekaru yana gudanar da aiki a kamfanin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng