Cin Hancin N1bn Ya Jawo Hon. Gudaji Kazaure Ya Tona Asirin Abin da ke Faruwa a CBN

Cin Hancin N1bn Ya Jawo Hon. Gudaji Kazaure Ya Tona Asirin Abin da ke Faruwa a CBN

  • Hon. Gudaji Kazaure ya fallasa adadin kudin da ke cikin kasafin kudin babban bankin Najeriya
  • A wata hira da aka yi da shi, Gudaji Kazaure ya tono abin da yake ganin badakala ce a bankin CBN
  • ‘Dan majalisar ya ce har mafi yawan abokan aikinsa a Majalisa ba su da masaniyar dawar garin

Abuja - A wata hira da aka yi da Muhammad Gudaji Kazaure a ranar Lahadi, ‘dan majalisar wakilan tarayyar ya jefi bankin CBN da laifuffuka da da-dama.

Muhammad Gudaji Kazaure ya halarci shirin fashin baki da Waziri Bulama Bukarti suke shiryawa, ya yi bayani kan kwamitinsu da ke binciken badakalar kudi.

‘Dan majalisar na jihar Jigawa ya zargi Gwamnan babban banki da yin kutun-kutun wajen ganin ‘dan jiharsa ya zama shugaban kwamitin kudi a majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Babban Banki Ya Koma Bakin Aiki, CBN Ya Fitar da Sabuwar Sanarwa

A dalilin wannan abin da Godwin Emefiele ya yi, Hon. Gudaji Kazaure ya ce ‘yan majalisa ba su iya binciken gwamnan da babban bankin duk barnar da ake yi.

‘Dan siyasar ya shaidawa shirin fashin baki cewa Godwin Emefiele ya saye duk manyan kasar nan.

CBN ya na ba manyan bashin Biliyoyi

Daga cikin hanyoyin da ake bi wajen rufe bakin masu mulki, Kazaure ya ce bankin CBN yana bada bashin da ya kai N2bn ba tare da an karbi kadarar mutum ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shi karon kan shi, ‘dan majalisar ya ce an yi masa tayin N1.8bn amma ya ki karba saboda tsoron kashe kudin, yace da ya karbi bashin nan da yanzu an saye shi.

CBN a Abuja
Taron manyan bankin CBN a Abuja Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Legit.ng Hausa ta ji Kazaure a hirar da aka yi da shi yana cewa ya san duk wani jami’i, gwamnati ko daidaikun mutanen da bankin CBN ya ba aron makudan kudi.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi: Emilokan Ba Musulmin Kwarai Bane - Melaye Ya Doke Tinubu a Gasar Karanta Fatiha

Daga N500bn a shekarun baya, sai da kasafin kudin CBN ya koma N1.3tr a shekarar 2022, yanzu kuwa Gudaji Kazaure ya ce bankin zai kashe N2.4tr a shekarar nan.

Yadda aka tilastawa Mukhtar Betara

Shugaban kwamitin kasafin kudi, Mukhtar Betara ya yi kokarin binciken kudin da ake warewa babban bankin, amma a cewar Kazaure, shugabanni suka tursasa shi.

Gudaji Kazaure yake cewa shi ma ya san da wannan labari ne saboda yana cikin kwamitin, ya ce ‘yan majalisar da ke masaniyar wannan a majalisa ba su kai 40 ba.

‘Dan majalisar ya ji labarin rikici ya barke tsakanin ‘yan kwamitin bayan shugabansu ya karbi cin hancin N1bn daga hannun gwamnan CBN, sai ya raba masu N10m.

Manyan masu kudin Najeriya sun yi gaba

An ji labarin cewa, wani rahoto na Oxfam ya nuna a cikin shekaru biyu zuwa uku, kusan 70% na kudin da suka shigo Najeriya sun kare ne a aljihun mutane 83.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fadi Wadanda Zai ba Mukamai da Abin da Zai Yi Kafin Kwana 100 a Aso Rock

Bincike ya nuna a duk ranar Allah, arzikin Attajiran Duniya yana karuwa da fiye da Naira Tiriliyan 1.2, a daidai lokacin da dubunnai suke neman abin da za su ci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng