Talaka na Murna, Kamfanonin Shinkafa na Tafka Asara saboda Karyewar Farashi
- Masu casar shinkafa sun bayyana damuwa kan yadda tsarin yafe harajin shigo da abinci ke jefa su cikin matsala
- Hukumar Kwastan ta bayyana cewa tsarin ya rage farashin kayan abinci da kashi 12 zuwa 18 cikin 100 a bana
- Kamfanoni sun ce shigo da abinci daga waje na kara kassara masana'antunsu da ma manoman cikin gida
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Masu aikin shinkafa a Najeriya sun koka kan yadda yafe harajin da gwamnati ta yi wa kayan abinci da ake shigo da su ke durkusar da harkokinsu na yau da kullum.
Wannan ya biyo bayan yanke hukuncin da gwamnatin tarayya ta yi na yafe harajin shigo da shinkafa, masara da dawa na tsawon kwanaki 150 domin rage tsadar abinci a kasa.

Asali: Getty Images
Punch ta wallafa cewa shirin ya fara aiki tun daga 15 ga Yuli zuwa karshen Disamba 2024, wanda ya shafi kayan abincin da suka hada da shinkafa, masara, wake da alkama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwastam ta ce farashin abinci ya ragu
Hukumar Kwastan ta bayyana cewa yafe harajin ya taimaka wajen saukaka farashin kayan abinci a kasuwa da tsakanin 12% zuwa 18%.
Shugaban hukumar, Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa kudin shigo da shinkafa da aka yafe ya kai kimanin Naira biliyan 45.9, yayin da na masara ya kai Naira biliyan 45.3.
Sai dai a yayin da gwamnati ke murna da saukar farashi, masana'antun nika shinkafa sun ce za su iya durkushewa sakamakon tsarin.
Babban manajan kamfanin Labana Rice Mill da ke Jihar Kebbi, Malam Alhassan Yusuf ya bayyana cewa gwamnati ta bayar da lasisin shigo da shinkafa ga wasu kamfanoni.
An fara rufe masana'antun shinkafa
Wani mai aikin shinkafa a unguwar Goru a jihar Kebbi, Abubakar Idris, ya ce ya rufe masana’antar sa saboda kayayyakin da ake shigo da su daga waje.
Ya ce:
“Farashin shinkafa ya fadi sosai, ba za mu iya gasa da na waje ba. Mun rufe masana’anta tare da sallamar ma’aikata.
"Muna fatan gwamnati za ta sake nazari don a farfado da masana’antun gida.”
Shi ma Alhaji Abubakar Bawa daga Kamba ya bayyana cewa masana’antarsa ta tsaya cak saboda kalubale da yawa da ba za su iya jurewa ba.
Daily Trust ta rahoto Alhaji Bawa ya ce:
“Lokacin mulkin Buhari ya kasance mafi alheri a gare mu. Amma yanzu shigo da shinkafar waje na kashe masana’antu.
"Muna bukatar gaggawar shirin gwamnatin tarayya don ceton wannan bangare.”

Asali: Getty Images
Masu casar shinkafa sun yi kira ga Tinubu
Masu casar shinkafa sun bukaci gwamnati da ta sake nazari kan tsarin yafe haraji da kuma bai wa masana'antun gida kariya.
Sun ce yayin da ake kokarin rage farashin abinci, ya kamata a duba tasirin hakan ga masana'antun cikin gida domin kada a lalata kasuwancin da aka dade ana ginawa.
'Yan kasuwa sun koka da saukar farashi
A wani rahoton, kun ji cewa masu boye abinci sun koka kan yadda farashin abinci ke karyewa a Najeriya.
Wasu 'yan kasuwa sun bayyana yadda suka ware makudan kudi suka saye kayan abinci iri iri amma farashi ya karye.
Legit ta rahoto cewa wani dan kasuwa ya bayyana yadda abokin shi ya ci bashin miliyoyin Naira ya saye abinci amma kasuwa ta juya masa baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng