Bichi: Abba Ya Kausasa Harshe da aka Zargi Kwankwaso da Karbar N2bn a Kudin Kano
- Abba Kabir Yusuf, ya karyata zargin da tsohon sakataren gwamnatin jihar, Dr Baffa Bichi ya yi cewa ana karkatar N2bn daga kudin jihar ana bai wa Rabiu Kwankwaso
- Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tsaftace duk wata harkar kudi, kuma babu wanda ke damfara ko karkatar da dukiyar al’umma kamar yadda aka yi zargi
- Abba ya ce zargin cewa Kwankwaso na karbar N2bn kowane wata ba shi da tushe, yana mai cewa Bichi yana son bata sunan wanda ya taba yi wa Kano da Najeriya hidima
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Abba Kabir Yusuf ya gana da kansiloli 484 da aka zaba daga mazabu na jihar Kano, a fadar gwamnatin jihar a ranar Lahadi da yamma.
A yayin ganawar, Abba Kabir Yusuf ya yi martani wa tsohon sakataren gwamnatin Kano, Dr Abdullahi Baffa Bichi kan zargin Sanata Rabiu Musa Kwankwso da babakere.

Asali: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa martanin na zuwa ne bayan wasu kalamai da aka danganta da Baffa Bichi inda ya zargi gwamnatin Abba bai wa Kwankwaso wasu kudi kowane wata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya ce Kwankwaso nada rikon amana
Gwamnan ya ce babu wani lokaci da Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi ko sisin kwabo daga gwamnatinsa.
Abba ya ce Kwankwaso ya taba zama gwamna har sau biyu, ya zama Sanata, Minista, dan majalisar wakilai da kuma dan takarar shugaban kasa, amma bai taba cin ko N1m ba.
The Nation ta rahoto ya ce bai kamata a raina mutum mai tarihinsa da jajircewarsa ba ko a nemi bata masa suna kawai saboda wani ya rasa mukami.
Gwamnan ya yi kira ga mutanen Kano da su ci gaba da riko da gaskiya da mutunta shugabanni, musamman wadanda suka bayar da gudunmawa wajen gina jihar da al’umma.
Abba ya zargi Bichi da kokarin jawo rabuwar kai
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Dr Baffa Bichi yana kokarin janyo rashin jituwa da rarrabuwar kai a cikin gwamnatin sa.
Ya ce zargin cewa ana karbo N2bn duk wata domin bai wa Kwankwaso ba shi da tushe, kuma ba za a yarda da Baffa Bichi ba tunda bai fadi hakan tun yana cikin gwamnati ba.

Asali: Twitter
Gwamnan ya ce duk wani mutumin kirki daga Kano ba zai fito ya raina jagororin da suka yi wa jihar aiki da rikon amana ba, kuma mutanen Kano ba za su lamunci haka daga kowa ba.
Abba Kabir Yusuf ya ce ana maraba da suka da gyara idan yana da tushe, amma ba za a yarda da cin mutunci da kage ga jagoran Kwankwasiyya ba.
Tafiyar Kwankwasiyya a Najeriya
Kwankwasiyya ta fara ne a matsayin tafiyar kishin kasa wadda ta samo ginshikinta daga hangen nesa na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya kafa tsarin ne domin cusa gaskiya, amana da aiki tukuru cikin matasa.
Wannan tsari ya yi fice wajen samar da dama ga dubban matasa ta hanyar ilimi, tallafin karatu zuwa kasashen waje, da kuma horar da su kan shugabanci da aikin gwamnati.
A karkashin wannan tafiya, an gina wata sabuwar al’ada ta shugabanci a Kano da ta mayar da hankali kan tsabtace makarantun gwamnati, sake farfado da asibitoci da samar da sabbin hanyoyi a matakin karamar hukuma da jiha.
Wannan tasiri ne da ke ci gaba da bayyana a yau, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ke samun karfin gwiwa daga irin tunanin jagororinsa na baya.
A ƙarkashin mulkinsa, an jaddada sake mayar da hankali kan walwalar al’umma da sake farfaɗo da masana’antu da gine-gine da suka rushe.
Ganin haka, da yawa daga cikin mabiya tafiyar Kwankwasiyya na kallon zargin almundahana da ake yiwa Kwankwaso a matsayin yunkuri na rage tasirin wani tafarki da ya riga ya kafa turbar sauyi a Kano.
Wannan ya sa har yanzu ake ɗaukar Kwankwasiyya a matsayin wata tafiyar mai karfi kuma mai tasiri wajen shirya makomar siyasar matasa da cigaban jihar gaba ɗaya.
Bichi ya zargi Abba da babakere a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa, tsohon sakataren gwamnatin Kano, Dr Abdullahi Baffa Bichi ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da almundahana.
Baffa Bichi ya ce barnar da aka yi a gwamnatin Abba Kabir Yusuf cikin shekaru biyu kacal ya wuce na gwamnatin Ganduje na shekaru takwas.
Tsohon sakataren gwamnatin na Kano ya bayyana cewa nan gaba kadan zai fito da bayanai da za su nuna gaskiyar maganganun da ya yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng