'Yan Bindiga Sun Kai Hare Haren Ramuwar Gayya a Zamfara, an Hallaka Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Kai Hare Haren Ramuwar Gayya a Zamfara, an Hallaka Bayin Allah

  • Ƴan bindiga sun ji zafin nasarar da dakarun sojoji masu aikin samar da tsaro suka samu a kansu yayin wani samame a jihar Zamfara
  • Miyagun sun huce fushinsu a kan bayin Allah, suka kai hare-haren ramuwar gayya a wasu ƙauyuka bakwai na ƙaramar hukumar Maru
  • Hare-haren sun jawo asarar rayuka yayin da kuma aka yi garkuwa da wasu mutane da ba a san adadinsu ba zuwa cikin daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun hallaka aƙalla mutane 12 a wasu hare-haren ramuwar gayya da suka kai a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun kuma sace wasu mutane da ba a san adadinsu ba a hare-haren da suka kai a wasu ƙauyuka da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun kashe mutane a jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga

Majiyoyi sun bayyana cewa harin, wanda ya faru a ranar 5 ga Mayu, 2025, da misalin larfe 1:30 na rana, na da nasaba da wani samamen da sojojin Najeriya na Operation Fansan Yamma suka kai a sansanin ƴan bindiga da ke dajin Dankurmi.

A ranar 3 ga watan Mayu, rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun hallaka fitattun ƴan bindiga guda biyar tare da ƙwato makamai a jihar Zamfara.

Samamen da ya gudana a yankunan ƙaramar hukumar Talata Mafara da Kaura Namoda, na daga cikin kokarin rundunar sojoji na fatattakar ƴan ta’adda da dawo da zaman lafiya a yankin.

Wannan farmaki ya yi sanadiyyar mutuwar ƴan ta’adda da dama, ciki har da jagorori guda biyar da suka haɗa da Auta Jijji, Dankali, Sagidi, Kachallah Rijaji da Kachallah Suza.

Ƴan bindiga sun farmaki ƙauyukan Zamfara

Majiyoyin sun bayyana cewa ƴan bindigan sun afka ƙauyuka guda bakwai a yankin Dankurmi da suka haɗa da Zamfarawa, Kurukuru, Dogon Daji, Dan Hayin Zamfarawa, Tungar Zabo, Burmukai da Dambawa.

Ƴan bindigan sun kashe mutane 12 sannan suka yi garkuwa da wasu waɗanda ba a san inda suka tafi da su ba.

'Yan bindiga sun yi barna a Zamfara
'Yan bindiga sun kashe mutane a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Bayan samun rahoton lamarin, sojoji da ke yankin sun fara ɗaukar matakin gaggawa yayin da ƙoƙarin ceto mutanen aka sace ke ci gaba da gudana.

Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga

Ƴan bindiga sun hallaka ƴan sa-kai

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a jihar Bauchi da ke yankin Arewa maso Gabas.

Ƴan bindigan sun hallaka mutum 11 ciki har da ƴan sa-kai a harin wanda suka kai a ƙauyen Mansur cikin ƙaramar hukumar Alkaleri.

Hakazalika miyagun sun sace tumakai da shanun mutane a ƙauyen Mansur da wasu ƙauyuka da ke makwabtaka da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng