'Yan Bindiga Sun Yi Artabu da Mafarauta a Sokoto, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Bindiga Sun Yi Artabu da Mafarauta a Sokoto, an Samu Asarar Rayuka

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi artabu da wasu mafarauta a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an hallaka mafarauta 11 a artabun da aka yi tsakaninsu da ƴan bindigan a cikin daji
  • Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da aukuwar harin ta hannun kakakinta, amma ba ta bayyana cewa an kashe mutum 11 ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Aƙalla mambobi 11 na ƙungiyar mafarauta sun rasa rayukansu sakamakon musayar wuta mai tsanani da ƴan bindiga a jihar Sokoto.

Musayar wutar ta auku ne tsakanin ɓangarorin biyu a ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.

'Yan bindiga sun kai hari a Sokoto
'Yan bindiga sun kashe mafarauta a Sokoto Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar The Punch ta rahoto cewa arangamar ta faru ne a ranar Juma’a, lokacin da mafarautan suka hana wasu ƴan bindiga kusan 40 kai hari a ƙauyen Magonho.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka fafata tsakanin mafarauta da ƴan bindiga

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ƴan bindigan, wadanda suka zo kan kusan babura 20, suna ɗauke da manyan makamai, sannan suka fara buɗe wuta bayan da aka hana su kai harin da suka shirya.

"Da farko, an tabbatar da mutuwar mafarauta biyu a farkon musayar wutar."
"Adadinsu ya ƙaru zuwa mutum 11 a ranar Asabar bayan jami'an tsaro sun gano wasu gawarwakin daga dajin da ƴan Lakurawa suke ciki."

- Wata majiya

Wani ganau ya bayyana cewa mafarautan sun taru cikin gaggawa bayan samun bayanan sirri kan motsin ƴan bindigan, inda suka yi nasarar daƙile harin farko da kuma ƙwato wasu daga cikin dabbobin da suka sace.

Ya ƙara da cewa, bayan janyewar ƴan bindigan sojoji daga sansanin Forward Operating Base da ke Masallaci sun bi sawunsu, inda suka ƙwato wasu daga cikin dabbobin da suka sace.

Sai dai ƴan bindigan sun sake dawowa ƙauyen Magonho bayan janyewarsu ta farko, inda suka ƙona ƙarfen sadarwa na MTN, sannan suka sake buɗe wuta a cikin ƙauyen kafin su tsere zuwa daji.

Majiyar ta tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin nemo gawarwakin sauran mafarautan da kuma gano waɗanda suka ɓace.

“Jami’an tsaro ciki har da sojoji da wasu daga cikin hukumomi daga Binji da Rakka na gudanar da aikin ceto a cikin dajin Lakurawa da ke da kauri.”

- Wata majiya

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Lokacin da Legit Hausa tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sanda jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar da harin da kuma ƙona ƙarfen sadarwa na MTN.

'Yan sanda
'Yan sanda sun tabbatar da harin 'yan bindiga a Sokoto Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter
"Eh, an samu rahoton hari a yankin da kuma ƙona ƙarfen sadarwa na MTN a ƙauyen."
"Ƴan Lakurawa sun hallaka mafarauta biyu yayin da suka shirya zuwa farauta a cikin daji."
"Mafarautan sun fito ne daga yankin Gwadabawa da ƙauyen Magonho."

- DSP Ahmed Rufai

Sojoji sun kashe ɗan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasara kan tsagerun ƴan bindiga a jihar Taraba.

Jami'an tsaron sun yi wa ƴan bindigan kwanton ɓauna ne bayan sun hango su suna kan hanyar kai farmaki a wani ƙauye.

Dakarun sojojin sun hallaka wani ɗan bindiga guda ɗaya ta fatattakar sauran a artabun da suka yi a cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng