Zamfara: Hatsabiban Ƴan Bindiga 5 Sun Baƙunci Lahira a Hannun Jami'an Tsaro

Zamfara: Hatsabiban Ƴan Bindiga 5 Sun Baƙunci Lahira a Hannun Jami'an Tsaro

  • Dakarun Runduna ta 1 a Najeriya sun hallaka manyan ‘yan bindiga a Zamfara, ciki har da Auta Jijji da Dankali a kokarin yaki da ta’addanci
  • Sojoji sun fafata da ‘yan bindiga a kauyen Mai Kwanugga a Talata-Mafara, inda suka kwato bindigogi da makamai masu linzami bayan kashe su
  • A wani lamari daban a Dayau, Kaura-Namoda, sojoji da ‘yan sanda sun shawo kan tarzoma da mazauna suka ta da saboda harin ‘yan bindiga a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar hallaka yan bindiga 5 da suka addabi al'umma.

Rundunar sojojin ƙarƙashin jagorancin Birgediya-Janar Timothy Opurum ta samu nasara wajen yakar ‘yan ta’adda a Zamfara da ke Arewa maso Yamma.

An hallaka ƴan bindiga 5 a Zamfara
Rundunar sojoji sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga a Zamfara. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

An hallaka manyan yan bindiga 5 a Zamfara

Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Kyaftin Suleiman Omale, ya fitar, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omale ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari kan mazauna gari da kona gidaje kafin zuwan dakarun a kauyen Mai Kwanugga.

Sanarwar ta ce:

"Lokacin da suka ci karo da su, sojojin suka fara fafatawa, inda suka hallaka manyan yan bindiga biyar masu hatsari."

Daga cikin ƴan bindigar da suka bakunci lahira akwai Auta Jijji, Dankali, Sagidi, Kachallah Rijaji, da Kachallah Suza.

Sojojin QRF da 1 BSF sun bi ‘yan bindigar da suka tsere, inda suka kwato bindigogi AK-47, 'PKT Machine Gun', da RPGs da harsasai.

A ranar 2 ga Mayu, yayin binciken bayan harin, mazauna yankin sun ba da bayanai da tabbatar da mutuwar wasu hatsabiban ‘yan bindiga.

Omale ya ce mutane biyu sun ji rauni sakamakon harbin bazata yayin artabu, amma an sa ido sosai don ganin an kakkabe sauran mayaƙan.

Yadda aka hallaka manyan yan bindiga 5 a Zamfara
Jami'an tsaro sun hallaka yan bindiga 5 a Zamfara. Hoto: Legit.
Asali: Original

Sojoji sun daƙile tarzoma a Zamfara

A ranar 1 ga Mayu, Omale ya ce dakarun CT2 tare da jami’an tsaro sun dakile tarzoma a Dayau da ke Kaura-Namoda.

Mazauna sun ta da zaune tsaye bayan hare-haren ‘yan bindiga, suka toshe hanya da tayoyi da kuma hana zirga-zirga a babban titin yankin.

Omale ya ce jami’an tsaro sun tarwatsa taron cikin lumana, suka dawo da zaman lafiya da bude hanyar, kuma komai ya koma kamar da.

Ya kara da cewa Birgediya-Janar Opurum ya yaba da jarumtar dakarun, ya kuma tabbatar da kudirinsu na dawo da zaman lafiya a jihar.

Omale ya bukaci jama’a su rika bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro, tare da kaucewa ɗaukar doka a hannunsu.

Yan bindiga sun hallaka limami a Zamfara

Mun ba ku labarin cewa 'yan bindiga sun kashe wani babban limami, Malam Salisu da wasu 'yan uwansa biyu da suka yi garkuwa da su wata biyu da suka wuce.

Malam Salisu da danginsa sun kasance a hannun 'yan bindigar ne tun wata biyu da suka gabata kafin a kashe su.

Lamarin ya tayar da hankali da kara jefa al'umma cikin fargaba da bakin ciki a yankunan da ake fama da rikici.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.