'Yan Bindiga Sun Kai Munanan Hare Hare a Sokoto, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Bindiga Sun Kai Munanan Hare Hare a Sokoto, an Samu Asarar Rayuka

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya
  • Ƴan bindigan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a hare-haren da suka kai cikin ƙauyuka guda uku
  • Miyagun dai sun riƙa shiga ƙauyukan ne ɗaya bayan ɗaya da yammacin ranar Juma'a, 2 ga watan Mayun 2025
  • Jami'an tsaro sun yi ƙoƙarin kai ɗauki zuwa ƙauyukan, amma sai dai kafin su isa ƴan bindigan sun tsere zuwa daji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kashe mutane 11 a wasu hare-hare da suka kai a jihar Sokoto.

Ƴan bindigan sun kashe mutanen ne a hare-haren da suka kai a ƙauyuka guda uku da ke cikin ƙananan hukumomin Gwadabawa da Sabon Birni na jihar Sokoto.

'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto
'Yan bindiga sun yi kashe-kashe a Sokoto Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai hare-hare a Sokoto

Majiyoyi na tsaro sun tabbatar da cewa mummunan lamarin ya auku ne a ranar Juma'a, 2 ga watan Mayu, da misalin ƙarfe 7:30 na yamma.

Ƴan bindigan da suka zo da yawa a kan babura sun fara harin ne a ƙauyen Satiru, inda suka buɗe wuta ba tare da ƙaƙƙautawa ba, suka kashe mutane biyar.

Bayan sun gama yin ɓarna a Satiru, sai suka wuce ƙauyen Kunkurus, inda suka kashe mutum ɗaya.

Amma hakan bai ishe su ba, domin daga nan sai suka nufi ƙauyen Shadawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni.

An nan ne suka sake bude wuta, suka kashe ƙarin mutane biyar, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da rudani.

Wannan hari ya sake bayyana yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a yankunan arewa maso yammacin Najeriya, musamman a jihar Sokoto da ke fuskantar hare-hare daga ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Jami'an tsaron Sokoto sun kai ɗauki

Domin martani ga waɗannan hare-hare, dakarun rundunar Operation Fansan Yamma tare da haɗin gwiwar rundunar ƴan Sandan Najeriya, hukumar NSCDC, da kuma rundunar tsaron Sokoto, sun tura jami’ansu zuwa yankunan da aka kai harin.

'Yan sanda
'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Dakarun sun bayyana cewa, zuwa lokacin da suka isa wuraren, ƴan ta’addan sun riga da sun tsere zuwa cikin dazuka.

A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da bin sahunsu domin kama su don fuskantar da su hukunci.

Al’ummar yankin na roƙon gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ɗaukar matakin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyi.

Ƴan binɗiga sun sace Basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani basarake zuwa cikin daji a jihar Benue.

Ƴan bindigan sun sace dagacin mai suna Dickson Idu a wani hari da suka kao a ranar talata, 29 ga watan Mayun 2025.

Tuni jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji da ƴan sanda suka bazama zuwa cikin daji domin ceto basaraken daga hannun miyagu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng