UTME 2025: Hanyoyi Mafi Sauki ga Dalibai don Duba Sakamakon Jarrabawar JAMB

UTME 2025: Hanyoyi Mafi Sauki ga Dalibai don Duba Sakamakon Jarrabawar JAMB

  • JAMB ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME ta 2025, inda ta ce dalibai miliyan 1.5 daga cikin 1,955,069 suka samu kasa da maki 200
  • Kididdigar ta JAMB ta nuna cewa dalibai 420,415 ne kawai suka samu sama da maki 200, wanda ke nufin 75% suka samu kasa da haka
  • Legit Hausa ta jero bayani dalla dalla kan hanyoyin duba sakamakon jarabawar ta yanar gizo da kuma ta hanyar aika sakon kar-ta-kwana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami’o'i (JAMB) ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME da dalibai suka zana a shekarar 2025.

A UTME ta wannan shekarar, fiye da dalibai miliyan 1.5 daga 1,955,069 da suka zana jarrabawar ne suka samu kasa da maki 200 a jarrabawar da aka kammala kwanan nan.

Hukumar zana jarabawar JAMB ta fitar da sakamakon UTME 2025, an ji yadda dalibai za su duba cikin sauki
Wata cibiyar zana jarabawar JAMB, inda aka ga dalibai na shirin fara zana jarabawar. Hoto:@JAMBHQ
Asali: Facebook

JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar UTME 2025

Wannan ya fito ne daga kididdigar sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2025 da hukumar JAMB ta fitar a ranar Litinin, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kididdigar ta nuna cewa dalibai 420,415 ne kawai suka samu maki sama da 200 a wannan jarrabawar ta 2025.

Bayanan sun nuna cewa kashi 75 cikin 100 na daliban sun samu kasa da maki 200, inda kasa da kashi 1 cikin 100 suka samu maki sama da 300.

Hukumar JAMB ta bayyana cewa ce an bai wa dalibai 40,247 da ba su kai shekaru 18 ba damar nuna bajintarsu, amma 467 (kashi 1.16%) ne kawai suka samu makin da ake bukata

An rahoto cewa an fara zana jarabawar UTME 2025 ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Afrilu.

Yadda ake duba sakamakon UTME 2025

A cikin wannan rahoto, Legit Hausa ta kawo matakan da dalibai za su bi domin duba sakamakon jarabawar UTME 2025 cikin sauki:

1. Duba sakamakon UTME 2025 ta yanar gizo:

Da farko a ziyarci shafin 'eFacility' na JAMB: Dalibi zai bude manhajar binciken intanet, misali, Chrome, sai ya ziyarci shafin hukumar JAMB a https://efacility.jamb.gov.ng/login.

Shigar da bayanai: Bayan shafin 'eFacility' ya bude, sai dalibi ya shigar da adireshin imel da kalmar sirri da kayi amfani da su lokacin rajista.

Duba sakamakon jarabawar: Bayan an bude shafin, sai a danna bangaren "Check UTME Results" don ganin makin UTME na kowane darasi da ka rubuta.

JAMB ta fitar da hanyoyi masu sauki ga dalibai domin duba sakamakon jarabawar UTME 2025
Dalibai suna zana jarabawar UTME a daya daga cikin cibiyoyin da JAMB ta amince da su. Hoto: @JAMBHQ
Asali: UGC

2. Duba UTME 2025 ta sakon kar-ta-kwana:

Da farko, dalibi zai bude manhajar aika sakonnin kar-ta-kwana: Sai ya shirya aika sako na SMS.

Rubuta sabon saƙo: A akwatin sakon, dalibi zai rubuta kalmar "RESULT" (da manyan haruffa) sannan ya rubuta bayansa da lambar rajistar JAMB ɗin a kasar kalmar.

Aika sako: Bayan an kammala rubutawa, sai a aika sakon zuwa ga 55019 ko 66019, lambobin hukumar JAMB don duba sakamakon.

Shigowar sako: JAMB za ta aiko maka da sako ɗauke da makin UTME na kowane darasi da ka rubuta. Amma za a caje ka N50 don aika wannan sako.

JAMB ta yi martani ga kalaman Peter Obi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, JAMB ta yi martani ga Peter Obi kan kalaman da ya yi game da tsarin jarrabawarta, inda ta ce tana fara jarrabawa ne da karfe 8:00 na safe.

JAMB ta musanta ikirarin Peter Obi na cewa tana fara jarrabawa da karfe 6:00 na safe, tana mai jaddada cewa karfe 8:00 na safe ne lokacin fara jarrabawarta.

Martanin JAMB ya zo ne bayan da Peter Obi ya nuna damuwarsa game da matsin da yara kanana ke fuskanta a kan barin gidajensu da Asubah don rubuta jarrabawar UTME.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.