Mun Yi Hankali: JAMB ta ki Bayyana Sunayen Wadanda suka fi Cin UTME a 2024

Mun Yi Hankali: JAMB ta ki Bayyana Sunayen Wadanda suka fi Cin UTME a 2024

  • Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB ta ce ba za ta bayyana wadanda su ka fi kowa maki a jarrabawar UTME ba
  • Shugaban hukumar na kasa, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan a Bwari dake Abuja a ranar Litinin din nan
  • Ya bayyana cewa su na son gujewa irin matsalar da ta afku a bara a kan wata daliba da ta bayyana sakamakon bogi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku.Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Hukumar shirya jarrabawar shiga makaratun gaba da Sakandare (JAMB) ta ce ba za ta bayyana wadanda su ka yi zarra a jarrabawar UTME da dalibai kimanin miliyan 1.9 su ka rubuta.

Kara karanta wannan

Hukumar shirya jarabawa JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME 2024

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da manema labarai a Litinin din nan a babban birnin tarayya Abuja.

Hukumar ta ki bayyana wadanda su ka yi zarra a sakamakon UTME
Kaso 70% na daliban sun samu maki kasa da 200 Hoto:Ishaq Oloyede
Asali: Facebook

Farfesan ya ce sun yanke shawarar kin bayyana sunayen wadanda su ka yi zarra ne domin gujewa irin dambarwar Mmesoma Ejimeke a bara, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mmesoma mai shekaru 19 ta bayyanawa duniya cewa ta samu maki 362 a jarrabawar UTME a shekarar 2023, amma daga baya aka gano maki 249 ta samu.

70% sun samu kasa da maki 200

Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya ce dalibai kimanin miliyan 1.94 ne su ka yi rajistar jarrabawar a cibiyoyi sama da 700 fadin kasar nan.

Ya ce cikin wannan adadi, kaso 70% sun samu kasa da maki 200 bayan an kammala makin sakamakon.

Kara karanta wannan

Shugaban hukumar JAMB, zai yi taro a kan sakamakon jarrabawar UTME 2024

Punch News ta wallafa cewa ana rubuta jarrabawar UTME ne saboda shiga makarantun gaba da sakandare, saboda haka babu dalilin bayyana wanda ya fi kowa maki.

Daliba ta hada sakamakon UTME na bogi

A baya mun kawo mu ku yadda wata daliba a jihar Anambra mai suna Mmesoma Ejikeme ta hada sakamakon UTME na bogi.

Dalibai mai shekaru 19 da ta yi ikirarin samun maki 362 ta tabbatarwa manema labarai cewa da kanta ta hada sakamakon.

Tun da fari, hukumar JAMB ce ta karyata sakamakon da Mmesoma ta ce ta samu, inda ta tabbatar da cewa maki 249 kawai ta samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel