Musa Kwankwaso Ya Faɗi Maƙarƙashiyar da Ake Shiryawa NAHCON, Sheikh Pakistan
- Jigon APC, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce ana kokarin dagula harkokin NAHCON da bata sunan shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman
- Ya bayyana cewa labaran da ake yadawa kan zaben ma’aikatan wucin gadi don aikin Hajjin 2025 ba su da tushe, kuma ba za a yarda da hakan ba
- Kwankwaso ya bukaci ‘yan jarida su rika neman gaskiya da kaucewa nuna bambanci, yana mai cewa an zabi kwamitin lafiya na Hajji a fili
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jigo a jam’iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi wasu zarge-zarge game da hukumar NAHCON.
Musa Kwankwaso ya zargi wasu da kaddamar da shirin bata sunan hukumar da shugabanta, Farfesa Abdullahi Usman Pakistan.

Asali: Facebook
NAHCON: Kwankwaso ya yi zargin makarkashiya
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon kwamishinan a mulkin Abdullahi Ganduje ya fadi haka ne yayin mayar da martani kan wani rahoto daga kafar labarai ta yanar gizo.
Rahoton ya zargi hukumar da nuna son kai wajen zaben ma’aikatan wucin gadi don aikin Hajjin shekarar 2025 da ke tafe a Saudiyya.
Sai dai Kwankwaso ya ce wadannan hare-haren ba su da tushe, kuma wani yunkuri ne na dagula NAHCON da karya shirin Hajjin 2025.
Ya bayyana cewa wannan lamari ba abin yarda ba ne, yana mai cewa duk wanda ke son ci gaban hukumar ya hada kai da shugaban domin dorewar nasara.

Asali: Facebook
Kwankwaso ya shawarci kafafen yada labarai
Kwankwaso ya bukaci kafafen yada labarai su kasance masu bin ka’idojin aikin jarida ta hanyar tantance gaskiya da nisantar son zuciya ko tsoma baki.
Sai dai Kwankwaso ya musanta rahoton da ke zargin magudi wajen zaben ma’aikatan wucin gadi da za su yi aikin Hajji a bana.
Kwankwaso ya ce:
“Abin ba zai yiwu ba wasu su dage kan dagula NAHCON karkashin Farfesa Abdullahi Sale Usman, ba za a lamunci haka ba.
"Ba sabon abu ba ne cewa shugaban ya kawo manyan sauye-sauye. Wadannan sauye-sauyen suna magance matsalolin da aka saba fuskanta a aikin Hajji.
"Amma wasu marasa kishin kasa suna son su rusa sauye-sauyen nan da kuma bata suna da mutuncin shugaban hukumar.
"Zaben kwamitin lafiya na kasa an yi shi a fili. An sanar da shi, mutane suka nema, sannan aka zabi wadanda suka cancanta.
Kwankwaso ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima bisa himmar su wajen ganin Hajjin bana ya tafi daidai.
Musa Kwankwaso ya soki Hakeem Baba-Ahmed
Kun ji cewa jigon APC, Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi martani kan sukar gwamnatin Bola Tinubu da Hakeem Baba-Ahmed da Buba Galadima suke yi.
Musa Kwankwaso ya ce mutanen biyu ba su isa su hana a sake zaɓen shugaban ƙasan ba a shekarar 2027.
Hon. Musa Kwankwaso ya nuna cewa yankin Arewa ba zai juyawa Tinubu baya ba, domin ya kawo masa ayyukan ci gaba.
Asali: Legit.ng