'SDP za Ta Wawushe Manyan 'Yan Siyasa,' El Rufa'i Ya Yiwa Jam'iyyarsa Albishir

'SDP za Ta Wawushe Manyan 'Yan Siyasa,' El Rufa'i Ya Yiwa Jam'iyyarsa Albishir

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya jinjinawa shugabancin jam’iyyar SDP da irin kokarinta na zama sabuwar madafar siyasa
  • El-Rufai ya bayyana cewa jam’iyyar SDP za ta samu karbuwa sosai kuma za ta taka rawa mai mahimmanci a babban zaɓe mai zuwa
  • Ya fadi haka ne a ziyarar da ya kai wa SDP ta reshen Kudu maso Gabas, inda ya samu tarbar karamcin daga manyan jam'iyyar a Enugu

Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Enugu – Tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ya kai wata muhimmiyar ziyara yankin Kudu maso Gabas a ranar Alhamis, 2 ga Mayu, 2025.

A yayin ziyarar, El-Rufa'i ya yabawa shugabancin SDP bisa kokarinsu wajen farfado da jam’iyyar da kuma gina wata sabuwar madafa ta siyasa da za ta zame wa Najeriya mafita.

Enugu
Tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufa'i ya ziyarci jagororin SDP a Kudu maso Gabas don karfafa jam'iyya Hoto: @officialsdp1
Asali: Twitter

Wani sakon da aka wallafa a shafin jam’iyyar SDP na X, ya bayyana cewa El-Rufa'i ya jinjinawa Alhaji Shehu Musa Gabam, shugaban jam’iyyar na ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da yaba wa 'yan kwamitin zartarwa na ƙasa (NWC), saboda kwazonsu da hangen nesa wajen tabbatar da ingancin jam'iyyar.

Nasir El Rufa'i a ziyarci Enugu

Ziyarar El-Rufa'i zuwa Enugu ta zo ne kwanaki kaɗan bayan irin ta da ya kai Kano, wanda ke ƙara haifar da hasashe game hade kan yan siyasa da El-Rufai ke kokarin yi gabanin zaɓen 2027.

Tsohon Ministan babban birnin tarayya Abuja, ya kara da cewa da yawa daga cikin ƴan Najeriya za su fara bin wannan tafiya nan ba da jimawa ba.

Kaduna
El-Rufa'i da wasu mayan SDP a ziyarar da ya kai Enugu Hoto: @officialsdp1
Asali: Twitter

A ziyarar, mataimakin shugaban jam’iyyar SDP na Kudu maso Gabas, shugabannin jam’iyya na jihohin yankin da wasu fmanyan yan siyasa sun tarbi El-Rufai da karamci.

Taron ya gudana cikin lumana inda El-Rufa'i ya ƙarfafa wa 'yan SDP guiwa da ƙara kwarin gwiwar aiki tare domin a kai ga ci.

Martanin jama'a ga ziyarar El-Rufa'i

Wasu daga cikin masu bibiyar SDP sun bayyana cewa ziyarar da El Rufa'i ya kai Enugu ba za ta haifar da 'da mai ido a yankin ba.

Magri Sanji ya rubuta cewa:

“Zai yi rashin nasara a Kudu. Mai tsattsauran ra’ayi ne, ba ya daraja rayuwar ɗan Adam. Jinin jihadin Shehu Dan Fodio na gudana a jikinsa. Za a ci gaba da ƙin amincewa da shi.”

Elder Olawale Desmond Oladipupo ya ce:

“Daga ƙarshe kuma ya shiga coci. 'Yan Najeriya suna gwagwarmaya da gaske."

Louis Pasteur ya ce:

“Aikin alheri guda ba zai iya wanke mugayen ayyukan mutum ba.”

Samuel Uche kuwa ya bayyana goyon bayansa da cewa:

“Madalla. Muna fatan ganin ƙarin irin wannan hadin kan siyasa.”

Nasir El-Rufa'i ya ziyarci Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana sabon ra’ayinsa dangane da tsarin karba-karba a shugabancin Najeriya a halin yanzu.

A wani abu mai kama da sauya ra'ayi, El-Rufa'i ya bayyana cewa abin da ya fi dacewa shi ne a duba cancanta, ba yankin da ɗan takara ya fito ba idan za a zabi shugaban kasa.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, inda suka tattauna batutuwa da dama na siyasa da makomar Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.