Tsohon Minista Tuggar Ya Soki Tinubu bayan Rasa Tikitin APC? An Ji Gaskiya
- Tsohon Ministan harkokin waje, Ambassada Yusuf Tuggar, ya yi martani kan rahotannin da ke cewa ya soki shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
- A cewar wasu rahotannin da aka yada, tsohon Ministan ya soki shugaban kasar ne bayan ya rasa.tikitin jam'iyyar APC
- Sai dai, a martanin da ya yi, ya warware zare da abawa kan rahotannin da aka yada a kansa masu nuna ya soki Shugaba Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Bauchi - Tsohon Ministan harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya sake jaddada goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu da manufofin gwamnatinsa.
Yusuf Tuggar ya yi watsi da rahotannin da ke cewa ya soki shugaban kasar a wata hira da ya yi kwanan nan.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Yusuf Tuggar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Abdulkadir Alkassim, ya fitar ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2026 a Bauchi.
Wane martani Tuggar ya yi?
Abdulkadir Alkassim ya ce an karkatar da kalaman da ya yi a wata hira da aka yi da shi da harshen Hausa, kuma an fassara su ba a muhallinsu ba.
“Don kauce wa shubuha, Ambasada Tuggar bai soki ko shakkar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kowace hanya ba. Duk wani labari akasin haka ƙarya ne kuma karkatar da kalaman nasa ne da gangan."
"Ministan ya kasance mai cikakken goyon baya da aminci ga shugaban kasar, kuma ya jajirce ga tsarin sabunta fata da kuma nasarar gwamnati mai ci ƙarƙashin jagorancin APC.”
- Abdulkadir Alkassim
Tuggar ya yi magana kan APC
A cewar sanarwar, kalaman Yusuf Tuggar a cikin hirar sun mayar da hankali ne a kan tsare-tsaren cikin gida na jam'iyyar APC a jihar Bauchi, musamman buƙatar gaskiya da adalci wajen zaɓen 'yan takara.
Ta bayyana cewa Tuggar ya ba da shawarar cewa ya kamata a bar mambobin jam'iyya su zaɓi 'yan takara cikin ƴanci ta hanyar tsari mai inganci da gasa ta gaskiya.

Kara karanta wannan
Da gaske Shugaba Tinubu ya yi ridda, ya fita daga addinin Musulunci? Gaskiya ta fito
Alkassim ya kuma ce Tuggar ya bayyana damuwarsa game da zargin wani ƙoƙari na yin katsalandan a tsarin zaɓen fitar da gwani na gwamna na APC a jihar, inda ya jaddada cewa ya kamata a bar masu neman takara su gwada farin jininsu a bainar jama'a.
“Abin da yake magana a kai shi ne cewa ya kamata dukkan masu neman takara su samu dama ta adalci domin shiga cikin gasa ta fili."
- Abdulkadir Alkassim

Source: Twitter
Tuggar na goyon bayan Tinubu
A cewar mai taimaka masa, Tuggar ya tabbatar da cewa kalaman nasa suna da nufin ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya na cikin gida a cikin jam'iyyar APC ne tare da haɓaka haɗin kai a jihar Bauchi.
“Ambassada Tuggar ya ginu daram a kan goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya jajirce ga haɗin kan jam'iyya, kuma ya sadaukar da kansa wajen ciyar da manufofin da ke kawo ci gaba, wadata, da kyakkyawan shugabanci gaba."
- Abdulkadir Alkassim
Gwamnatin Tinubu ta yi gargadi
A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi gargadi mai zafi game da zaben shekarar 2027 inda ta zargi wasu da shirin kawo fitina.
Gwamnatin Bola Tinubu ta zargi wasu ‘yan siyasa da ba a bayyana sunayensu ba da yunƙurin amfani da addini wajen harkokin siyasa kafin zaɓen 2027.
Ta ce za a gano waɗannan ‘yan siyasa tare da kai su ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike da ɗaukar mataki.
Asali: Legit.ng
