A karshe, ISWAP Ta Dauki Alhakin Dasa Bam da Ya Kashe Mutane 26 a Borno
- Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta fito ta dauki alhakin dasa bam din da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 26 kusa da garin Rann, jihar Borno
- Wani jami’in tsaro ya ce wasu gawarwakin sun kone kurmus ta yadda ba za a gane su ba, yayin da aka ce mata da yara sun mutu a harin
- Rahoto ya nuna cewa ISWAP da Boko Haram na kara kai hare-hare a Arewa maso Gabas duk da ikirarin gwamnati na cewa an ci galaba kan su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Kungiyar ISWAP ta dauki alhakin fashewar bam da ta auku a kusa da garin Rann, a karamar hukumar Kala-Balge da ke jihar Borno.
Legit Hausa ta ruwaito cewa abin fashewar ya tarwatse ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a, a yankin Furunduma, ya hallaka mutane 17 nan take.

Asali: Getty Images
Mutane 26 sun mutu a fashewar bam
Bayan faruwar lamarin, an gano cewa daga cikin wadanda suka mutu, akwai mata hudu, yara shida da wasu fasinjoji bakwai, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai daga bisani an gano karin gawarwaki a dajin da ke kewaye da wurin fashewar, lamarin da ya kai yawan wadanda suka mutu zuwa 26 a ranar Litinin.
Wani jami’in tsaro da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa wasu daga cikin gawarwakin sun kone sosai, ta yadda ba za a iya gane su ba.
ISWAP ta dauki alhakin harin Borno
Kwatsam kuma sai ga shi a ranar Talata, ISWAP ta wallafa sanarwar daukar alhakin harin a shafin Telegram, inda ta tabbatar da mutuwar mutane 26, a cewar rahoton.
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ba ta fitar da wata sanarwa ba a halin yanzu dangane da harin da kuma ikirarin ISWAP na daukar nauyin harin.
Wani rahoto daga kungiyar International NGO Safety Organisation ya nuna cewa, wata mota ce ta taka bam a kan hanyar da ke tsakanin Rann da Gamboru Ngala.
Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna jerin gawarwakin da aka nannade cikin farar leda a dakin ajiyar gawa na asibitin Rann.

Asali: Original
Karuwar tashin hankali a Arewa maso Gabas
Kungiyoyin ISWAP da Boko Haram na ci gaba da fafatawa da jami’an tsaro a yankin Arewa maso Gabas, su na amfani da bama-bamai domin kai wa fararen hula da jami’an tsaro hari
Yakin Boko Haram ya shafe sama da shekaru 15 yana addabar yankin, ya hallaka fiye da mutane 40,000.
Duk da cewa gwamnati ta ce an ci galaba kan kungiyoyin, har yanzu dai 'yan ta'addan na ci gaba da kai hare-hare a garuruwan yankin.
ISWAP na da babban sansani a Arewacin Borno, inda take kai hari ga ayarin motoci da kuma dasa bama-bamai a kan hanyoyi, kamar yadda rahoton Al Jazeera ya nuna.
Fashewar bam din ranar Litinin na cikin sababbin hare-hare da ke tayar da hankali a yankin, inda rahotanni suka nuna cewa a ‘yan kwanakin nan mutum fiye da 50 suka mutu.
Sojoji 2 sun mutu a wani fashewar bam
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojoji biyu sun mutu a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, bayan da suka taka wani bam da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka dasa.
Rahotanni daga jami’an tsaro da mazauna yankin sun ce fashewar ta auku ne kusa da kauyen Nyeliri da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno.
Hakazalika, Hakimin Damboa, Alhaji Lawan Maina, ya tabbatar da lamarin, ya na mai cewa sojoji biyu ne suka rasa rayukansu a fashewar bam din.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng