An kai Hari Mai ban Tsoro kan Masu Jana'iza a Borno, an Kashe Mutane
- 'Yan ta'adda sun kai farmaki yayin jana'izar wani mutum a ƙauyen Kwaple, Chibok, inda suka kashe mutum 15
- Rahotanni sun nuna cewa sun kona coci da gidaje fiye da biyar, tare da yin garkuwa da jama’a masu yawa
- Shugaban ƙaramar hukumar Chibok ya tabbatar da faruwar harin, amma 'yan sanda ba su ta fitar da cikakken bayani ba tukuna
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai farmaki a ƙauyen Kwaple da ke kusa da karamar hukumar Chibok a jihar Borno.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kashe mutane 15 tare da yin garkuwa da wasu da dama.

Asali: Original
Punch ta wallafa cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe 7:00 na dare a ranar Litinin, a daidai lokacin da jama’ar yankin ke cikin gudanar da jana’izar wani dan ƙauyen da ya rasu a baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban karamar hukumar Chibok, Modu Mustapha, ya tabbatar da aukuwar harin, yana mai cewa harin ya auku ne a lokacin da jama’a ke cikin jana’iza.
Boko Haram sun kashe 15 ana jana'iza
Wani mazaunin yankin da aka kai harin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa manema labarai cewa:
“Harin ya kasance tamkar mafarki mai ban tsoro. Duk da ban halarci jana’izar ba, bayanai sun tabbatar min da cewa mutane 15 ne suka mutu — yawancinsu maza ne.”
Ya ƙara da cewa:
“’Yan ta’addan sun kona cocin EYN da ke yankin, sun kuma kona gidaje kusan guda biyar da wasu kadarorin al’umma.”
Lamarin ya sake jefa al’ummar Chibok da kewaye cikin firgici da fargabar tsaro, musamman ganin cewa yankin na daga cikin wuraren da Boko Haram ke kai hare-hare tun 2014.
Yadda aka kai hari Borno cikin dare
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun dura ƙauyen ne cikin dare yayin da mutane ke cikin alhini da addu’o’in jana’iza. Sai suka fara harbe-harbe a iska kafin su afka cikin taron jama’a.
Wani da ya tsira daga harin ya bayyana cewa:
“Sun shigo ne da manyan bindigogi, suka fara harbi ba kakkautawa. Mutane suka watse, wasu suka shiga jeji, wasu kuma ba su samu tsira ba."
Yanzu haka, an ce ana cigaba da tantance yawan wadanda suka bace da kuma asarar dukiyoyi da aka yi sakamakon harin.

Asali: Facebook
An yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso, amma bai ɗauki wayar ba kuma bai kira ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
An kai wa makiyaya hari a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa wani shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar Filato ya tabbatar da cewa an kai musu wani hari.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe shanu 37 da bindiga yayin da aka kai wa makiyaya harin.
Sai dai shugaban makiyayan ya ce sun yi kira ga 'yan uwansu da kada su dauki doka a hannu kasancewar sun sanar da hukuma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng