An Gano Kuskuren da Ya Jawo Atiku Abubakar Ya Fadi Zaben 2023 a PDP
- Sanatan Binuwai ta Kudu, Abba Moro ya ce PDP za ta ci zaben 2023 da ba a zabi Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar ba
- Ya bayyana zabin Okowa a matsayin babban kuskure da ya hana PDP samun nasara a jihar Delta duk da tasirin da jam'iyyar ke da shi a can
- Sanatan ya zargi Okowa da rashin jajircewa ga jam’iyyar PDP, yana cewa bai ba da cikakken goyon baya, ko wani hobbasa a zaben da ya gabata ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Sanata mai wakiltar mazabar Binuwai ta Kudu, Abba Moro, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP za ta iya lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Sai dai ya ce PDP ta tafka kuskuren zabar tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin mataimakin dan takara ga Atiku Abubakar.

Asali: Facebook
Sanatan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Channels Television a shirin a ranar Talata, sa’o’i bayan Okowa ya bayyana nadamarsa na yin tafiya da Atiku Abubakar a zaben 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘An yi kuskuren takarar Okowa/Atiku,’ Sanata
The Cable ta wallafa cewa Sanata Abba Moro ya bayyana zabin Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin dan takarar PDP a zaben 2023 a matsayin babban kuskure.
Ya ce furucin Okowa da ya nuna nadama bayan kasa bai wa jam’iyyar PDP nasara a jiharsa ta Delta, alama ce da ke nuna cewa zuciyarsa ba ta tare da jam’iyyar.

Asali: Facebook
Sanata Moro ya ce:
“Idan aka duba abubuwan da suka faru yanzu, da bayanan da muke da su, wasu daga cikinmu na ganin PDP za ta lashe zaben da an zabi wani dan takara daga Kudu banda Okowa a matsayin mataimakin Atiku.”
Sanata Abba Moro ya caccaki Ifeanyi Okowa
Sanata Moro ya kara da cewa bai dace tsohon gwamna Okowa ya samu bakin magana ba, ganin yadda ya kasa cicciba jam'iyyar ta ci zaben 2023.
Ya ce:
“Ta yaya za a bayyana wannan al’amari da cewa gwamna mai ci a lokacin, tsohon Sanata kuma mataimakin dan takarar shugaban kasa bai iya kawo jiharsa ga jam’iyyarsa ba?”
“Kuma idan aka duba, Sanatoci biyu daga jihar Delta daga jam’iyyun adawa ne, ba PDP ba. Don haka ina ganin zabin Okowa a 2023 babban kuskure ne.”
Sanata Moro ya ce dukkannin abubuwan da suka biyo baya bayan zabin Okowa na nuni da rashin jajircewa da kuma cikakken goyon baya ga jam’iyyar PDP daga bangarensa.
Okowa ya yi magana kan sauya shekar Atiku
A baya, kun samu labarin cewa tsohon gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa, ya bayyana cewa Atiku Abubakar na dab da barin jam’iyyar PDP. da ya yiwa takara a zaben 2023.
Okowa ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi a ranar Talata, inda ya bayyana cewa Atiku yana nazarin ficewa daga PDP, kuma yana dab da ɗaukar mataki a kan wannan shawara.
Sanata Okowa ya kuma tabbatar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki tare da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP daga jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng