Bayan Bindige Shanu 37 a Filato, Amurka Ta Shiga Harkar Makiyaya a Najeriya

Bayan Bindige Shanu 37 a Filato, Amurka Ta Shiga Harkar Makiyaya a Najeriya

  • Jakadan Amurka Richard Mills ya gana da shugabannin Miyetti Allah domin jin korafe-korafen makiyaya
  • An tattauna batun rashin tsaro da hanyoyin da za a bi domin warware rikice-rikicen da ke faruwa cikin lumana
  • Martani daga jama’a ya banbanta, wasu sun yabawa taron, wasu kuma sun soki ganawar da ake ganin ta daɗa ɓata lamarin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jakadan Amurka a Najeriya, Ambasada Richard Mills, ya gana da shugabannin kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN).

Rahotanni sun nuna cewa sun gana ne domin jin ƙorafe-ƙorafen da ke damun makiyaya a ƙasar nan.

Amurka
Jakadan Amurka ya gana da kungiyar Miyetti Allah a Abuja. Hoto: @UsinNigeria
Asali: Twitter

Legit Hausa ta tattaro bayanai kan ganawar ne a cikin wani sako da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amurka ta gana da kungiyar Miyetti Allah

Taron da aka gudanar ya shafi muhimman batutuwa kamar yadda za a rage tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma da kuma neman hanyoyin kawo zaman lafiya mai ɗorewa.

An bayyana cewa ganawar wani bangare ne na ƙoƙarin diflomasiyyar Amurka don fahimtar ainihin tushen matsalolin tsaro da suka addabi yankunan karkara a Najeriya.

Bashir Ahmad ya yaba da ganawar

Daya daga cikin wadanda suka yi martani kan wannan ganawa shi ne, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari Bashir Ahmad.

A wani sakon da ya wallafa a X, Bashir ya bayyana farin cikinsa kan yadda Amurka ta yarda ta gana da Miyetti Allah duk da wasu na ƙoƙarin ɓata sunan kungiyar.

A cewarsa:

"Duk da cewa wasu na ƙoƙarin yi wa Miyetti Allah laƙabi da kungiya mai alaƙa da ta’addanci, har yanzu gwamnatin Amurka ta ci gaba da yi musu kallon halastacciyar kungiya.

"Ina fatan wannan zai kawo ƙarshen tuhumar da ake musu."

Bashir ya kara da cewa hakan ya nuna cewa Miyetti Allah na da muhimmanci a batun samar da zaman lafiya da shawo kan rikicin makiyaya da manoma.

Shanu
Amurka na duba hanyoyin rage rikicin makiyaya a Najeriya. Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

David Hundeyin ya soki ganawar

Sai dai wani dan jarida mai zaman kansa, David Hundeyin, ya bayyana rashin jin daɗinsa da ganawar.

Hundeyin ya zargi Miyetti Allah da zama ƙungiya da ke da alaka da haddasa rikice-rikicen kisan manoma a Najeriya.

A sakon da ya wallafa a X, Hundeyin ya ce:

"Menene alakar jakadan Amurka da wakilan wata ƙungiya da ke ɗaukar alhakin hare-haren da ke kashe manoma a Najeriya?
"Idan ku na ganin babu wata mummunar manufa a wannan ganawa, ku bayyana dalilin hakan."

Hundeyin ya ce akwai alamun wata ɓoyayyar manufa da Amurka ke yi a nahiyar Afrika, musamman ganin irin ƙungiyoyin da suke bai wa muhimmanci a tattaunawa.

An bindige shanu 37 a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Miyetti Allah ta sanar da bindige shanu har 37 a wani hari da aka kai musu a Filato.

Shugaban kungiyar a yankin da aka kai harin, Ibrahim Yusuf Babayo ya ce an kai musu harin ne da bindigogi.

Baya ga haka, shugaban ya bayyana cewa sun sanar da sojoji, 'yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki domin a bi musu hakkinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng