An kai Hari kan Makiyaya a Filato, An Bindige Shanu 37 har Lahira
- Wasu mutane da ba a san ko su wane ba sun harbe shanu 37 a yankin Tashek a ƙaramar hukumar Riyom a jihar Filato, kamar yadda MACBAN ta bayyana
- Wannan hari na zuwa ne mako guda bayan makamancin haka a unguwar Tanjol inda makiyaya biyu suka jikkata kuma aka kashe shanu guda biyar
- Shugaban MACBAN na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya ce an sanar da hukumomin tsaro kuma ana jiran matakin da za su ɗauka kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau - Rahotanni daga jihar Filato na nuna cewa an sake kai hari kan makiyaya a ƙaramar hukumar Riyom, inda aka kashe shanu 37.
An kai harin ne a unguwar Tashek a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 1:00 na rana, kamar yadda shugaban MACBAN na jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar.

Asali: Getty Images
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan lamari na zuwa ne mako guda bayan wani hari da aka kai a unguwar Tanjol inda aka jikkata makiyaya biyu tare da kashe shanu guda biyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zargi maharan da neman kawo rikici
Ibrahim Yusuf Babayo ya bayyana cewa an kai harin ne ba tare da makiyaya sun tsokani wasu mutane ba, yana mai cewa lamarin wani ƙoƙari ne na bayyana ɓoyayyar manufar kawo ruɗani.
Ya bayyana cewa 'yan bindigar sun farmaki shanun da ke kiwo sannan suka fara harbi, inda hakan ya yi sanadin kashe shanu 37 da jikkata wani makiyayi.
Hakan na zuwa ne yayin da rikici ya fara lafawa a jihar Filato bayan wasu hare hare da aka kai a kwanakin baya.
Makiyaya sun sanar da jami'an tsaro
Shugaban MACBAN ya ce bayan faruwar lamarin, ya sanar da kwamandan Operation Safe Haven (OPSH) na yankin Riyom, wanda ya tura jami’an tsaro zuwa wurin da abin ya faru.
Babayo ya kara da cewa ya tuntubi kwamandan sashen OPSH, GOC 3, kwamishinan 'yan sanda na jihar da kuma Daraktan Tsaro na Jiha (SDS) domin sanar da su.
Gargadi kan daukar doka a hannu
Ibrahim Yusuf Babayo ya jaddada cewa duk da irin waɗannan hare-hare, ya bukaci makiyaya su kasance masu haƙuri tare da gujewa ɗaukar doka a hannunsu.
Ya ce sun riga sun dogara da hukumomin tsaro da fatan za su kama waɗanda suka aikata wannan laifi tare da kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare.
Jihar Filato dai ta shafe shekaru tana fama da hare hare da ke da alaka da kabilanci, addini da sauransu.

Asali: Getty Images
An kama masu safarar makamai a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da kama masu safarar makamai da masu garkuwa da mutane.
Rahotanni sun nuna cewa cikin wadanda aka kama akwai wani jami'in tsaro mai safarar makamai da ba a bayyana sunan shi ba.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yaba da kokarin da hukumar DSS take a jihar wajen kama masu laifi da kawo zaman lafiya.
Wanda ya tantance Ibrahim Yusuf, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng