Gwamna Ya Soki Peter Obi bayan Rahoton Talauci a Najeriya Ya Jawo Sukar Tinubu
- Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya zargi Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP a 2023, da jawo wa jiharsa talauci a lokacin ya na gwamnan Anambra
- Wannan na zuwa ne a matsayin martani ga kalaman Peter Obi bayan ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu a kan rahoton cewa za a samu karuwar talauci a Najeriya
- Sanwo-Olu ya bayyana cewa bayan Peter Obi ya bar mulki, Willie Obiano, wanda ya gaje shi, ya rage talauci a jihar Anambra daga fiye da 60% zuwa 14.8%
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya mayar da martani ga Peter Obi, kan zarginsa game da rahoton talauci a karkashin mulkin Bola Tinubu.
Wannan ya biyo bayan sukar da Obi ya yi bayan rahoton da ke yin hasashen cewa za a samu karuwar talauci a Najeriya daga yanzu zuwa shekarar 2027 a karkashin mulkin Tinubu.

Asali: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa, a lokacin da yake magana a Jami'ar Johns Hopkins, Obi ya ga laifin gwamnatin tarayya a kan karuwar talauci a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Legas ya soki Peter Obi
The Guardian ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa, Sanwo-Olu ya bayyana cewa Obi ba shi da bakin da zai caccaki wansu a kan maganar karuwar talauci.
Sanwo-Olu ya bayyana cewa talauci ya karu a lokacin da Obi ke mulkin jihar Anambra, yana mai cewa:
“A lokacin da Peter Obi yake gwamnan Anambra na zangon mulki biyu, talauci a Anambra ya karu. Bai ragu ba.
Kafin Peter Obi ya zama gwamnan Anambra a ranar Alhamis, 14 ga Yuni, 2007, matsalar talauci a Anambra tana 41.4%. Amma bayan shekaru biyu kawai a ofis, talaucin a Anambra ya tashi zuwa kashi 53.7%.”
‘An samu ci gaba bayan mulkin Obi,’ Gwamna
Sanwo-Olu ya ce shekaru biyar da Peter Obi ya bar ofis, magajinsa, Willie Obiano, ya rage yawan talauci a Anambra daga kusan 60% zuwa 14.8%.”

Asali: Twitter
Ya ci gaba da cewa:
“Saboda haka, ba na ganin cewa Mista Obi yana da bakin magana a wajen yin irin waɗannan zargi da ya yi kan Najeriya a Jami’ar Johns Hopkins.”
Ya kuma bayyana cewa Obi ya taimaka wajen ƙara yawan talauci a Najeriya, yayin da Tinubu a matsayin gwamnan Legas ya dauke miliyoyin mutane daga talauci.
Jigon PDP ya ba Peter Obi shawara
A wani labarin, kun ji cewa jigo a jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya shawarci tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, da ya bar jam’iyyar da ya ke ciki, yakuma koma PDP kafin 2027.
Sowunmi ya bayyana cewa wannan mataki ne zai taimaki Peter Obi, tare da jaddada cewa zai taimaka shi wajen cimma bukatarsa na yin jagoranci a Najeriya a babban zabe mai zuwa.
Ya ce idan shi ne Obi, da ya koma jam’iyyar PDP domin neman tikitin takarar shugaban kasa, sai dai shawararsa na zuwa a lokacin da tsohon dan takarar ya shiga hadakar Atiku.
Asali: Legit.ng