Kisan Mutane 150 Ya Girgiza Peter Obi, Ya Buƙaci Tinubu Ya Katse Abin da Ya Je Yi a Faransa

Kisan Mutane 150 Ya Girgiza Peter Obi, Ya Buƙaci Tinubu Ya Katse Abin da Ya Je Yi a Faransa

  • Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Mista Peter Obi ya bayyana damuwarsa kan taɓarɓarewar tsaro a wasu jihohin da ke Najeriya
  • Obi ya yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya katse duk abin da yake yi a Farasa, ya dawo Najeriya don fuskantar matsalar
  • Ya ce a ƴan kwanakin nan da ƴan ta'adda suka zafafa kai hare-hare, an yi asarar rayuka sama da 150 musamnan a Zamfara, Borno da Filato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - 'Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta dakatar da abin da yake a ƙasar Faransa.

Mista Obi ya buƙaci Shugaba Tinubu ya katse zaman da yake a ƙasar Faransa ya dawo Najeriya domin funkantar matsalar tsaro da ke ƙara ƙamari a baya-bayan nan.

Obi da Tinubu.
Peter Obi ya bukaci Shugaba Tinubu ya hanzarta dawowa gida saboda matsalar tsaro Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana hakan a shafinsa na X da yake martani kan munanan hare-haren da aka kai jihohin Zamfara, Filato da Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hare-hare sun karu da Tinubu ya tafi Faransa

A ƴan makonnin da suka shige, hare-haren 'yan bindiga da ayyukan ta’addanci ya kara yawa musamman a jihohin Filato, Zamfara, Borno da wasu sassan kasar nan.

Duk wannan abu da ke faruwa, wanda ya jawo asarar rayuka fiye da 150, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na kasar Faransa da ke nahiyar Turai.

Tun a ranar 2 ga Afrilu ne Tinubu ya bar Najeriya zuwa Faransa domin wani abin da aka bayyana a matsayin “ziyarar aiki ta makonni biyu”.

Peter Obi ya koka da yanayin tsaro

Sai dai Obi ya bayyana cewa tafiyar ta zo a lokacin da Najeriya ke cikin matsanancin halin rashin tsaro da ya kamata shugaban kasa ya tsaya ya fuskanta.

Tsohon gwamnan ya ce ya zama wajibi ya yi kira ga Shugaban ƙasa ya katse wannan tafiya, ya dawo gida domin magance ayyukan ta'addanci da ke ƙaruwa.

“A cikin makonni biyu da ka shafe a waje, fiye da mutane 150 sun mutu saboda matsalar tsaro a sassan kasar nan, musamman a jihohin Filato da Zamfara,” in ji Obi.
Peter Obi.
Peter Obi ya ce matsalar tsaron Najeriya abin damuwa ne Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Twitter

Obi ya bukaci Tinubu ya dawo Najeriya

Ya kara da cewa ta'addanci a sake dawowa a Borno, hare-haren ’yan ta’adda a Kudu maso Gabas, da fashewar bututun mai a yankin Neja Delta sun nuna cewa Najeriya na cikin halin kaka-ni-kayi.

“Duk da wannan hali da ake ciki, shugaba kwata-kwata watau CEO na kamfanin da ake kira Najeriya ya sa ƙafa ya tafi wata ƙasa, ya bar asalin hedkwatar kamfaninsa."

- In ji Peter Obi.

Obi ya bukaci shugaban kasa ya gaggauta datse duk abin da yake yi a Faransa, ya dawo gida domin shawo kan matsalolin da ke addabar al’umma.

"Ana fama da yunwa" - Peter Obi

A wani labarin, kun ji cewa Peter Obi ya koka kan halin yunwa da fatara da ƴan Najeriya ke fuskanta a ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda abubuwa ke ƙara taɓarɓarewa da yadda mutane ƙe ƙara talaucewa a ƙasar nan.

Ya ce halin da aka shiga ya kai ga mutanen da suka taimake shi a baya, sun dawo suna neman ya taimaka masu da abin da za su ci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262