An Kama Ango da Abokansa kan Jawo Mutuwar Amarya wajen Huldar Aure

An Kama Ango da Abokansa kan Jawo Mutuwar Amarya wajen Huldar Aure

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wani ango da abokansa bisa zargin hannu a mutuwar amaryarsa kwanaki bayan bikin aurensu
  • Rahotanni sun ce ango da wasu abokansa uku sun kutsa cikin ɗakin amarya da niyyar tilasta mata hulɗar aure, lamarin da ya janyo rasuwarta
  • Kwamishinan ‘yan sanda ya umarci a mika binciken zuwa sashen CID na jihar domin zurfafa bincike da shirin gurfanar da su a gaban kotu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Wani lamari mai tayar da hankali ya auku a ƙaramar hukumar Sule Tankarkar ta jihar Jigawa inda ya jawo mutuwar wata amarya.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin wani ango da hannu a mutuwar amaryarsa kwanaki kaɗan bayan aurensu.

Lawan Shiisu Adam
An kama ango bayan mutuwar amarya a Jigawa. Hoto: Lawan Shiisu Adam
Asali: Facebook

Kakakin rundunar 'yan sanda jihar Jigawa, SP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar wa Legit faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton da rundunar ‘yan sanda ta fitar ya nuna cewa angon, tare da wasu abokansa uku, sun kutsa cikin ɗakin amaryar da nufin tilasta mata hulɗar aure ba da yardarta ba.

An ruwaito cewa rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama dukkan waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.

Baya ga kama su, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP AT Abdullahi, ya bayar da umarnin mika lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na jihar.

An zargi ango da jawo mutuwar amarya

Rundunar ta bayyana cewa a ranar 26 ga Afrilu, 2025 da misalin ƙarfe 10 na dare, ofishin ‘yan sanda na Sule Tankarkar ya samu rahoton mutuwar wata amarya.

Binciken farko ya nuna cewa angon mai suna Auwal Abdulwahab mai shekara 20 ya gayyaci abokansa domin kokarin shawo kan amaryarsa.

Abokan na shi da ake zargi da hannu a mutuwar amaryar su ne Nura Basiru, Muttaka Lawan da Hamisu Musa, mazauna kauyen Tungo.

An tabbatar da mutuwar amarya

Bayan samun rahoton, DPO na yankin tare da tawagarsa suka garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka dauki gawar amaryar zuwa Asibitin Gumel domin bincike.

Bayan isa asibitin, likita ya tabbatar da mutuwar amaryar, kuma an mika gawarta ga iyayenta domin gudanar da jana’iza kamar yadda addini ya tanada.

Za a mika ango da abokansa kotu

BBC Ta wallafa cewa wamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarni cewa a mika batun zuwa State CID dake Dutse domin gudanar da bincike mai zurfi domin tattabar da adalci.

Rundunar ta tabbatar da cewa bayan kammala bincike, za a gurfanar da angon da abokansa a gaban kotu bisa zargin haɗin baki da kuma kisan kai.

Yan sanda
Ana bincike bayan amarya ta mutu a jihar Jigawa. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Rarara ya angwance da Aisha Humaira

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya angwance da Aisha Humaira bayan daura musu aure a jihar Borno.

Yayin da yake bayyana farin cikin shi a kan auren, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa ranar na cikin muhimman ranaku a rayuwar shi.

A nata bangaren, Aisha Humaira ta ba mutane hakuri bisa rashin sanarwa da gayyatar daurin auren, tana mai cewa an je saka rana ne sai aka yanke shawarar daurin auren.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng