Allahu Akbar: Bidiyon mutuwar amarya ana tsaka da liyafar aurenta a jikin angonta

Allahu Akbar: Bidiyon mutuwar amarya ana tsaka da liyafar aurenta a jikin angonta

  • Bidiyon wata amarya da ta rasu ana tsaka da liyafar bikinta da angonta ya tada hankalin jama'a ba kadan ba
  • A bidiyon mai cike da tausayi, an ga angon ya riko amaryar amma kwatsam sai ta kubce ta fadi kasa jikinta ya saki
  • Tuni 'yan biki suka fara tururuwar garzayawa wurin da masoyan suke wadanda mutuwa tayi wa shigar sauri

Wani bidiyo mai matukar tada hankali ya bayyana a kafar sada zumuntar zamani na Instagram inda aka ga mutuwar amarya ana tsaka da shagalin liyafar aurenta kuma tana hannun mijinta.

A bidiyon da @naija_trending_ suka wallafa a shafnsu na Instagram, an ga amarya da angon zaune a kujera da farko. angon ya rungumo amaryarsa amma sai ta rinjaye shi suka fadi kasa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda na asirce mijina, babu wacce ta isa ta kwace min shi, Matar aure ta sanarwa duniya

Amarya ta mutu
Allahu Akbar: Bidiyon mutuwar amarya ana tsaka da liyafar aurenta a jikin angonta. Hoto daga @_naija_trending
Asali: Instagram

Tuni jama'a 'yan biki suka fara tururuwar zuwa inda suke yayin da jikin amarya ya saki ta fadi kasa kuma angon ya bi ta.

Tsokacin Naija Trending din shi ne: "Jama’a mu ji tsoron Allah, Domin ba wanda ya san lokacin mutuwar sa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Latsa nan don kallon bidiyon.

Jama'a sun yi martani

@__maamarhh tace: "Wannan abu akwai kunar rai, wayyo Allah."
@maimuna_isah: "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun Tabbas shi ne Allah.... Mutuwa bai da lokaci. Allah yasa mu yi kyakyawan karshe."

Zargin cin amana: Hotunan magidanci da ya sheke matarsa, ya mika kansa hannun 'yan sanda da muhimmiyar shaida

A wani labari na daban, Magidanci mai shekaru 55 ya sheke matarsa mai shekaru 45 bayan ya zargeta da cin amanarsa kuma daga bisani yayi tafiyar kusan kilomita 12 zuwa ofishin 'yan sanda da kanta.

Kara karanta wannan

Bidiyon yara 3 da aka tsinta suna gararamba a titin Edo wurin karfe 11 na dare

Lamarin ya faru ne a Chandrasekharpur dake yankin Odisha Dhenkanal a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 15 ga watan Yulin 2022.

Bidiyon mai matukar ban tsoro na mutumin yana tafe da kan matarsa da ya sheke ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani.

'Yan sanda sun kama wanda ake zargin yayin da yake tafe da cirarren kanta zuwa ofishin 'yan sanda dake yankin Dhenkanal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel