Innalillahi: Amarya ta rasu a ranar da aka daura auren ta kafin a kai ta dakin miji

Innalillahi: Amarya ta rasu a ranar da aka daura auren ta kafin a kai ta dakin miji

  • Abun al'ajabi da tashin hankali ya auku a wani gidan biki da ke garin Kano sakamakon mutuwar amarya bayan daurin auren ta
  • Kamar yadda Gen Sunus ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya sanar da cewa amarya Hannatu Yahaya ta rasu kafin a kai ta gidan mijin ta
  • Kamar yadda katin daurin auren ya nuna, an daura auren wurin karfe 11 na ranar Asabar, 27 ga watan Nuwamba da masoyin ta Isyaka Yusuf

Kano - Daga Allah mu ke, kuma gare shi za mu koma. Labarin da ke iso mana shi ne na rasuwar wata amarya mai suna Hannatu Yahaya.

Ba rasuwar bace sabon abu, yadda al'amarin ya kasance ne ya dimauta jama'a masu tarin yawa.

Innalillahi: Amarya ta rasu a ranar da aka daura auren ta kafin a kai ta dakin miji
Innalillahi: Amarya ta rasu a ranar da aka daura auren ta kafin a kai ta dakin miji. Hoto daga Gen Sunus
Asali: Facebook

Kamar yadda fitaccen ma'abocin amfani da kafar sada zumunta ta Facebook, Gen Sunus ya wallafa a shafinsa, ya sanar da cewa ta rasu ne bayan an daura aurenta kafin a kai ta gidan mijin ta.

Kara karanta wannan

Bidiyo da hotunan Jaruma Laila ta cikin shirin Labarina yayin da ta yi aure

Kamar yadda wallafar tace:

"Innalillahi-wa-inna-ilaihi-raj'un. Ya Allah ka gafarta wa 'yar uwa Hannatu Yahaya. An daura auren ta jiya kuma Allah ya karbi ran ta a jiyan kafin ta tare a gidan mijin ta."

Kamar yadda katin daurin auren ya nuna, lamarin ya auku a garin Kano ne bayan daura auren Hannatu Yahaya da masoyin ta Isyaka Yusuf a ranar Asabar da ta gabata.

Babu shakka wannan lamarin ya tashi hankalin jama'a inda aka dinga kwararawa amarya marigayiya Hannatu addu'o'in rahamar Ubangiji tare da dangana ga masoyin ta kuma angon ta.

Mai yankan kauna: Rasuwar angon Disamba ta tada hankulan ma'abota Facebook

A wani labari na daban, jama'a masu tarin yawa sun kadu tare da shiga matukar tashin hankali a kafar sada zumuntar Facebook sakamakon rasuwar matashi Sani Ruba.

Kara karanta wannan

Kotu ta haramta wa EFCC gurfanar da Dickson, ta ce CCB sun tantance kadarorinsa

Duk da kowanne mai rai mamaci ne kuma rashi ya saba taba mutane, rashin Sani Ruba ya gigita jama'a ne ganin ranar 11 ga watan Disamba mai zuwa zai angwance.

Labarin mutuwar matashin mai shekaru talatin da shidan ta bazu ne bayan wacce zai aura, Rafeeah Zirkarnain ta wallafa a shafin ta na Facebook.

A sanarwar ta: "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Masoyi na Sani Ruba, ashe ba za mu kasance mata da mijin ba a ranar 11 ga watan Disamba... Tun jiya na ke jin wani iri amma na cire tunanin a rai na... Ba zan taba samun mutum irin ka ba a matsayin miji."

Asali: Legit.ng

Online view pixel