Jerin Jihohi 5 da Aka Roƙi Tinubu Ya Yi Gaggawar Sanya Dokar Ta Ɓaci bayan Rivers

Jerin Jihohi 5 da Aka Roƙi Tinubu Ya Yi Gaggawar Sanya Dokar Ta Ɓaci bayan Rivers

Wasu kungiyoyi, cibiyoyi har ma da jam'iyyun PDP da APC sun yi ta kiran a sanya dokar ta-ɓaci a wasu jihohi saboda matsaloli daban-daban da ke damun su.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ana kiran Bola Tinubu ya sanya dokar saboda kokarin dakile abubuwa munana da ka iya biyo baya duba da mafi yawan jihohin na fama da matsalar tsaro.

An bukaci Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a wasu jihohi
Jerin jihohin da aka bukaci Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci bayan daukar matakin a Rivers. Hoto: Fr. Alia Iormen Hyacinth, Asiwaju Bola Tinubu, Dauda Lawal.
Asali: Facebook

Jihohin da aka bukaci dokar ta-ɓaci

Jaridar Punch ta ce daga jihohin da ake kiran Tinubu ya dauki matakin dokar ta-ɓaci sun fito daga Kudanci da kuma Arewacin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta yi bincike kan jihohin da aka bukaci Tinubu ya ƙaƙaba dokar ta-baci saboda wasu dalilai.

1. Jihar Kano

APC ta yi barazana ga gwamnatin Kano wurin kiran Bola Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci game da zargin matar shugabanta, Abdullahi Umar Ganduje.

Jam'iyyar ta yi barazanar saboda kalaman Mataimakin gwamna, Kwamred Aminu Abdulsalam Gwarzo kan Hafsat Ganduje.

Mataimakin gwamnan ya zargi matar tsohon gwamnan Kano kuma shugaban APC na yanzu da badakalar kuɗin fansho.

Gwarzo ya ƙara da kiranta 'gwaggwon matsiyata', lamarin da ya fusata ƴan APC har ta fara batun a ƙaƙaba wa Kano dokar ta ɓaci kamar a Rivers.

Sukar matar Ganduje ya jawo matsala a Kano
An taso wasu gwamnoni a gaba kan bukatar sanya musu dokar ta-ɓaci. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: UGC

2. Jihar Zamfara

Wata ƙungiyar Arewa ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a jihar Zamfara saboda tabarbarewar tsaro.

Kungiyar CAJ ta zargi gwamnatin Zamfara da yin salon mulkin 'kama karya' yayin da ta ce jihar ba ta samun wani ci gaba a yanzu.

NCAJ ta ce garuruwa sun koma biyan haraji ga ‘yan bindiga, jami’an gwamnatin jihar na amfana da haramtacciyar hakar ma’adinai.

3. Jihar Benue

Cibiyar CJI, mai fafutukar tabbatar da adalci ta bukaci Bola Tinubu ya ƙaƙaba dokar ta-baci a jihar Benue.

Cibiyar ta yi ƙorafi kan halin da jihar Benue ke ciki musamman na rashin tsaro da kullum ake hallaka al'umma.

Sai dai Gwamna Hyacinth Alia ya yi fatali da masu kiran gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ganin irin halin da ake ciki a yau, cewar Channels TV.

Alia ya ce babu wani dalili da ya kai a ayyana dokar ta ɓaci, ya na mai cewa wasu ƴan siyasa ne ke kokarin fakewa da hakan don cimma burinsu.

Ya buƙaci cibiyar CJI da ta gabatar da hujjoji a bainar jama’a ko kuma su fuskanci sakamakon wannan karya da ta ƙirƙiro mara tushe balle makama.

An taso gwamna a gaba kan kiran sanya dokar ta-ɓaci
Jihohin da aka bukaci Tinubu ya ƙaƙaba musu dokar ta-ɓaci a Najeriya. Hoto: Fr. Alia Lormen Hyacinth.
Asali: Twitter

4. Jihar Ondo

A jihar Ondo kuwa, jam’iyyar PDP ta yi barazanar neman dokar ta-baci idan Gwamna Aiyedatiwa ya kasa magance matsalar tsaro mai tsanani.

Jam'iyyar ta zargi gwamnati da yin shiru a matsalar tsaro, tana mai cewa ana kashe manoma da sace mutane ba tare da daukar mataki ba.

Kakakin jam'iyyar, Leye Igbagbo ya ce gwamnati na nuna kamar babu wata matsala, duk da cewa rayukan mutane na salwanta a kowane lungu na jihar.

Daga bisani, PDP ta ce ya dace Bola Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar kamar yadda ya yi a Rivers da rigimarsu ba ta kai haka ba.

5. Jihar Osun

Tsohon ministan harkokin ‘yan sanda, Oyewale Adesiyan, ya bukaci a ayyana dokar ta-baci a Osun saboda tabarbarewar tsaro da rikicin siyasa.

Adesiyan ya zargi Gwamna Ademola Adeleke da kin bin umarnin kotu, yana mai cewa hakan ne ya haddasa rikicin kananan hukumomi da asarar rayuka.

Ya bukaci a yi amfani da Sashe na 305 na kundin tsarin mulki don tabbatar da doka da oda tare da dawo da zaman lafiya a Osun.

Yadda aka taso wasu gwamnoni kan dokar ta-ɓaci
Jihohin da aka bukaci Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Asiwaju Bola Tinubu, Dauda Lawal.
Asali: Facebook

Mata sun fito zanga-zanga a Rivers

Mun ba ku labarin cewa wasu mata a Jihar Rivers sun gudanar da zanga-zangar lumana domin goyon bayan dokar ta-baci da Bola Tinubu ya ayyana a jihar a watan Maris 2025.

Wannan ne karon farko da aka samu gangamin goyon bayan wannan mataki, inda matan suka soki Simi Fubara tare da neman a tabbatar da zaman lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa matan sun bayyana cewa tun bayan ayyana dokar ta-baci, jihar ta samu sauƙin rashin tsaro da rage ayyukan ‘yan ta’adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.