'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Wani Mummunan Hari da Suka Kai a Sokoto
- Miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a wani ƙauyen da ke ƙaramar hukumar Rabbah ta jihar Sokoto
- Ƴan bindigan sun hallaka mutum ɗaya tare da raunata wani mutum ɗaya a harin da suka kai ranar Lahadi da daddare
- Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce ba ta san adadin mutanen da ƴan bindigan suka sace ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari a garin Rarah da ke cikin ƙaramar hukumar Rabbah a jihar Sokoto.
Ƴan bindigan waɗanda suka kai harin a ranar Lahadi, sun kashe mutum ɗaya tare da sace wasu mutane da dama.

Asali: Twitter
Yadda ƴan bindigan suka kai harin
Jaridar The Punch ta ce majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ƴan bindigan sun afkawa garin ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyin sun ce ƴan bindigan sun kai harin ne jim kaɗan bayan wata gobara ta tayar da hankulan mutanen ƙauyen.
Ƴan bindigan ɗauke da makamai daga zuwansu sai suka buɗe wuta ba kakkautawa, inda suka yi awon gaba da mutane da dama kafin su fice daga ƙauyen.
Mutane na cikin firgici a ƙauyen Sokoto
Mutanen yankin sun nuna fargaba da takaici kan yawaitar irin waɗannan hare-hare, inda suka roƙi gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakin da ya dace cikin gaggawa.
Wani mazaunin garin mai suna Bashar Lauwali ya bayyana cewa suna rayuwa ne cike da tsoro da fargaba.
"Rayuwarmu cike take da tsoro, muna jin harbe-harbe a ko ina kuma ba mu san ko za mu ga wayewar gari ba."
- Bashar Lauwali
Ya ƙara da cewa, baya ga asarar rayuka, hare-haren da ake kai wa sun lalata tattalin arziƙin yankin, mutane da yawa ke fama da yunwa tare da nema kuɗin fansa don ceto ƴan uwansu da aka sace.
An miƙa koken ƴan bindiga ga gwamnati
Duk da koke-koken da suka sha yi, mazauna yankin sun ce babu wani jami’in gwamnati ko na tsaro da ya je yankin domin duba halin da suke ciki.
"Muna kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya, da kuma hukumomin tsaro su gaggauta ɗaukar mataki kafin lamarin ya ƙara taɓarɓarewa."
"Muna buƙatar ƙarin jami’an tsaro, da kuma ɗaukar mataki mai tsauri kan waɗanda ke aikata wannan aika-aika. Haka kuma, muna neman tallafi ga iyalan da abin ya shafa.
- Bashar Lauwali
Ƴan sanda sun yi ƙarin haske kan lamarin
Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Kakakin ƴan sandan ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa an kashe mutum ɗaya tare da raunata wani mutum ɗaya.
Ya bayyana cewa babu haƙiƙanin adadin mutanen da aka sace domin da ƴan bindigan suka zo, mutane sun arce zuwa cikin daji.
"Eh gaskiya ne lamarin ya auku. Sun kashe mutun ɗaya tare da raunata wani mutum ɗaya.
Babu takamaimai bayani kan adadin mutanen da aka sace domin wasu sun gudu zuwa daji da ƴan bindigan suka shigo."
- DSP Ahmed Rufai
Ƴan bindiga sun kai hari a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma.
Ƴan bindigan ɗauke da miyagun makamai a yayin harin sun hallaka mutum biyu tare da yin awon gaɓa da wasu mutane zuwa cikin daji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng