Filayen jirgin saman Najeriya suna daga cikin masu muni a duniya, in ji wata hukuma

Filayen jirgin saman Najeriya suna daga cikin masu muni a duniya, in ji wata hukuma

- Hukumar kula da jiragen sama na kasa da kasa ta fidda sunayen tashoshin jiragen sama masu inganci

- Hukumar ta fidda sunayen wasu kasashen a cikin jerin, sai dai ba a sunan fili ko daya ba na Najeriya

- Hakan ya bayyana munin filayen jiragen Najeriya, FAAN kuwa ta bayyana tana kokarta inganta filayen

Ya tabbata cewa, filayen jiragen sun kasance a matsayi mara kyau na yawancin filayen jiragen saman Najeriya wanda ke ci gaba da jawo Allah-wadai daga matafiyan Najeriya, Nigerian Tribune

Hukumar Kula da Filin Jirgin Sama ta Kasa da kasa (ACI) ta fidda jerin filayen jiragen sama guda 29 a duk fadin Afirka wadanda suka dace da ma'aunin kiwon lafiya na kungiyar ta duniya.

A cikin sabon shirin ACI na Kula da Kiwon Lafiya na Filin Jirgin Sama (AHA), filayen jiragen sama 29 daga Afirka sun sami babbar takardar shaidar tabbatar da filin jirgin saman Kasa da Kasa sai dai babu ko daya daga filayen jiragen saman da ke Najeriya.

KU KARANTA: Watanni 5 bayan turawa Rarara kudade, har yanzu batun wakar Buhari shiru

Filin jiragen saman Najeriya suna daga cikin masu muni a duniya, in ji wata hukuma
Filin jiragen saman Najeriya suna daga cikin masu muni a duniya, in ji wata hukuma Hoto: X-Plane.org
Asali: UGC

Daga cikin filayen jirgin saman da aka amince da su sun hada da: Kotoka International Airport, Ghana, Diori Hamani International Airport, Niger, Filin jirgin saman Kigali, Rwanda, Aeroport Dakar Blaise Diagne Airport, Senegal da Maputo International Airport, Mozambique.

Sauran kasashen Afirka wadanda hukumar ta duniya ta amince da filin jirgin su sun hada da; Jamhuriyar Benin, Cape Verde, Masar, Guinea, Morocco, Afirka ta Kudu, Tunisia da Madagascar.

A cikin wani hanzari na martani, mai magana da yawun Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Sama na Nijeriya (FAAN), Misis Henrietta Yakubu ta bayyana cewa:

“muna ci gaba da kokarinmu na inganta kayan aiki a duk filayen jirginmu don tabbatar da matukar jin dadi ga duk masu amfani da filin jirgin.
"FAAN na aiki tukuru don rufe duk gibin da aka bude a wasu don a yarda da su tare da sauran filayen jirgin saman Afirka."

KU KARANTA: Gwamnati ta daskare asusun bankin Sunday Igboho, ya yi martani

A wani labarin, Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya ce, Najeriya za ta bukaci samar da guraben aiki miliyan 5 a kowace shekara har tsawon shekaru 10 don cike gibin rashin aikin yi, Premium Times ta ruwaito.

A cikin wani rahoto a ranar Litinin, asusun ya ce samar da wannan adadin ayyukan zai cimma burin kirkirar ayyuka da suka kai miliyan 54 a cikin shekaru goma masu zuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.