Gwamnatin Uba Sani Ta Warware Aikin El Rufa'i, An Kwace Gidaje a Kaduna
- Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya kwace filaye da gidaje a harabar makarantun gwamnati da aka raba a mulkin Nasir El-Rufa'i
- A sanarwar da gwamnatin Kaduna ta fitar, ta ce za ta mayar da filayen don amfanin jama’a da inganta ilimi ba tare da cikas ba
- Sanarwar da sakataren gwamnatin jihar, AbdulKadir Muazu Meyere ya fitar ta ce tuni aka sanar da mutanen da abin ya shafa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayar da umarnin kwace wasu gidaje da filaye da gwamnatin baya ta raba a cikin harabar makarantu a jihar.
Wannan matakin ya shafi makarantu irin su Alhuda-Huda College da ke Zariya da kuma Queen Amina College da ke garin Kaduna.

Asali: Facebook
Bayanin kwace filayen na kunshe a sanarwar da Sakataren gwamnatin jihar, AbdulKadir Muazu Meyere ya fitar, wacce Fatima Ajia Muhammad, ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce matakin kwace filayen ya samu amincewa tun shekarar da ta gabata, kuma tuni an sanar da wadanda aka saida wa filayen.
Kaduna: Gwamnati ta yi bayani kan kwace filaye
The Guardian ta ruwaito cewa gwamnatin ta ce an kwace filayen ne da nufin dawo da su don amfanin jama’a da kuma kare makarantun da samun damar fadada su.
Government Commercial College da ke Zariya na daga cikin wuraren da gwamnatin ta kwace filayensu bayan gwamnatin Nasir El-Rufa'i ta sayar da su a baya.

Asali: Twitter
Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin jihar na daukar matakan dawo da kudin da aka biya ga waɗanda suka sayi gidajen, kamar yadda gwamnan jihar ya bayar da umarni.
A cewar Uba Sani:
“Mafi kyawun yanayi na karatu shi ne wanda babu cikas ko hayaniya daga waje. Daya daga cikin matakan farko da na dauka bayan na hau mulki shi ne rage kudin makarantu a manyan makarantu na jihar Kaduna a ranar 21 ga Agusta, 2023.”
Sauyin Ilimin da gwamnatin Kaduna ta kawo
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa tana gudanar da manyan ayyuka a fannin ilimi, ciki har da gina rijiyoyi 51 a makarantu daban-daban a fadin jihar.
Haka kuma an samar da bandakuna 918 don malamai da ɗalibai., sai gina sababbin ajujuwan karatu 2,336, da gyaran wasu ajujuwan karatu 707.
Sanarwar ta kara da cewa an kuma samar da kayan karati 3,704 ga malamai da kuma 30,742 ga ɗalibai domin tabbatar da samun ci gaba a makarantun Kaduna. A cewarta, wannan na daga cikin burin gwamnatin Uba Sani na tabbatar da ingantaccen ilimi tare da samar da yanayi mai dacewa da karatu a duk fadin jihar.
Kaduna: Uba Sani ya magantu kan El-Rufa'i
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya yi magana a kan yawan masu sukar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da wasu ke yi
Ya bayyana cewa masu yin hakan, kamar tsohon gwamnan, Nasir El-Rufa'i, ba wai suna sukar ne don ci gaban ƙasa ba, illa domin burin samun mulki saboda kansu.
Uba Sani ya ce kokarin da wasu ke yi na kafa hadakar ‘yan adawa domin kifar da gwamnatin Tinubu ba zai kai ga nasara ba, kuma lokaci ya yi da yan Najeriya za suwaye.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng