Abin Fashewa Ya Tarwatse, Ya Kashe Yara 2 a Kaduna? 'Yan Sanda Sun Gano Gaskiya

Abin Fashewa Ya Tarwatse, Ya Kashe Yara 2 a Kaduna? 'Yan Sanda Sun Gano Gaskiya

  • Rundunar 'yan sandan Kaduna ta karyata labarin fashewar bam a yankin Abakpa, tana mai cewa bindigar mafarauta ce kawai ta tashi
  • Lamarin ya faru ne da safiyar Talata a titin Josawa, inda tashin bindigar ya jawo mutuwar wani yaro dan shekara 12, Abubakar Muhammed
  • Rundunar ta ce tana gudanar da bincike domin gano yadda aka samu tashin bindigar, tare da jan kunnen jama'a kan yada labaran karya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta karyata rahotannin da ke cewa an samu fashewar bam a yankin Abakpa da ke cikin birnin Kaduna.

A cewar sanarwar rundunar, an samu kuskuren tashin wata bindigar Baushe ne, wanda hakan ya jawo mutuwar yaro ɗan shekara 12.

Rundunar 'yan sanda ta fitar da rahoto kan batun tshin bam a Kaduna da ya kashe yaro dan shekara 12
Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

'Yan sanda sun karyata 'tashin bam' a Kaduna

ASP Mansir Hassan, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ya fitar da wannan bayani a ranar Talata kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa binciken farko na sashen yaki da bama-bamai ya tabbatar da cewa bindiga ce aka harba, ba fashewar bam ba kamar yadda ake ta yadawa.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar Talata a kan titin Josawa da ke unguwar Abakpa, jihar Kaduna, a cewar ASP Mansir.

Tashin bindiga ya kashe yaro, ya raunta wasu 7

Rahotanni sun tabbatar da cewa, sunan yaron da ya rasu Abubakar Muhammed, mai shekaru shekara 12, ya na zama da iyayensa ne a titin Josawa.

Haka kuma, rundunar 'yan sanda ta ce mutane bakwai sun samu raunuka daban-daban a lokacin da bindigar ta tashi.

ASP Hassan ya ce:

“Rahoton farko daga masana na sashen bama-bamai ya tabbatar da cewa ba fashewar bam ba ce, bindigar mafarauta ce ta tashi.”

Ya ce DPO na ofishin Kawo ya jagoranci wata tawagar hadin gwiwar jami’an DSS da shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa zuwa inda abin ya faru.

'Yan sanda suna gudanar da bincike mai zurfi kan tashin bindigar baushe da ya kashe yaro a Kaduna.
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP), Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

'Yan sanda za su zurfafa bincike a Kaduna

ASP Hassan ya bayyana cewa ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi domin gano ainihin musabbabin fashewar bindigar da kuma inda aka same ta.

The Nation ta rahoto rundunar 'yan sandan ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da bai wa jama’a sahihan bayanai da zarar bincike ya kara zurfi.

Sanarwar ta roki jama’a da su guji yada jita-jitar labaran da ba a tabbatar da ingancinsu ba domin kauce wa tayar da hankula.

Rundunar ‘yan sandan ta ce tana jajantawa iyalan marigayin kuma za ta tabbatar da adalci da hukunta masu hannu a lamarin.

An samu asarar rayuka a jihar Kaduna

Tun da fari, mun ruwaito cewa, wani abi fashewa ya tashi a jihar Kaduna, kuma ya yi sanadin mutuwar mutane a ranar Talata, 22 ga Afrilu, 2025.

An ce abin fashewar ya yi sanadin mutuwar yara biyu; ɗaya ɗan shekara 13, ɗaya kuma mai shekaru shida, lamarin da ya tayar da hankulan jama’a.

Bayan haka, wasu mutum uku sun samu raunuka sakamakon fashewar da har yanzu ba a gano musabbabinta ba, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.