Cin hanci: An kama wani jami'in 'yan sanda da aka gani bidiyo yana shin karbar cin hanci

Cin hanci: An kama wani jami'in 'yan sanda da aka gani bidiyo yana shin karbar cin hanci

  • Rundunar 'yan sanda ta kama wasu jami'ai da ake zargi da karbar cin hanci a wajen masu ababen hawa a kan hanya
  • Wani bidiyo da aka yada a Twitter ya nuna lokacin da wani jami'i ke cacar baki da wani mai abin hawa domin ya bashi kudi
  • Ana yawan samun jami'an 'yan sandan Najeriya da shiga harkar rashawa da cin hanci a bakin aikinsu

Jihar Edo - Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta cafke wani dan sanda mai suna Victor Osabuohign aka dauka a wani faifan bidiyo da aka yana ciniki da wani maia bin hawa da nufin karbar kudi a hannunsa.

ASP Jennifer Iwegbu, mataimakiyar jami’in hulda da jama’a na rundunar ne ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a Benin ranar Juma’a, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

Ms Iwegbu ta ce an kama jami’in, an tsare shi kuma a halin yanzu ana gudanar da bincike akansa.

An kama wani jami'i da ke karbar rashawa
Cin hanci: An kama jami'in 'yan sanda a cikin bidiyo na karbar kudi | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Ta ce rundunar ta kafa wani kwamitin wucin gadi karkashin jagorancin ACP James Chu, shugaban ayyuka na rundunar domin gudanar da binciken.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ms Iwegbu ta ce Provost Marshal na rundunar, CSP Avanrenren Godwin, shi ne mataimakin shugaban kwamitin da aka kafa.

Ta kuma ce akwai wasu jami’an da aka kama a baya bisa zargin cin hanci wanda ake ci gaba gudanar da bincike a hukumance akansu.

Ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abutu Yaro, ya bukaci jama’a da su kai rahoton jami’an da aka gani suna saba dokar aikinsu.

Hakazalika, wani rahoton jaridar Punch ya ce jami'ai bakwai ne ya zuwa yanzu rundunar ke kan bincika da irin wannan laifi.

Dan sanda Ya Kashe Wasu ‘Yan Bindiga 2 da Suka Kai Hari Gidansa

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Yan Arewa Mazauna Jihar Imo Tare da Filewa Mutum Daya Kai

A wani labarin, an kashe wasu ‘yan bindiga biyu a ranar Alhamis yayin da suka kai hari a gidan wani sufeton ‘yan sanda a garin Orogwe garin da ke a karamar hukumar Owerri ta Yamma a jihar Imo, a kudu maso gabashin Najeriya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Michael Abattam ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, amma bai bayyana sunan sufeton ‘yan sandan ba, Premium Times ta ruwaito.

Ya ce ‘yan bindigar sun tsallake shingen gidansa ne kana suka shiga harabar gidan inda suka lalata masa kofa, amma sufeton ‘yan sandan ya yi dauki ba dadi dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel