Jami'an yan sanda 200,000 ke tsaron manyan mutane kadai - Tsohon IGP na yan sanda
- Tsohon Sifeton yan sanda, Solomon Arase, ya fasa kwai
- Ya ce yan sandan Najeriya masu kudi kadai suke tsaro, maimakon daukacin yan Najeriya
Tsohon Sifeto Janar na yan sanda, Solomon Arase, ya ce sama da yan sanda 200,000 ake baiwa manyan yan siyasa maimakon tsaron al'ummar Najeriya milyan 200.
Ya bayyana hakana a jawabin da yayi a tattaunawar makarantar koyar da ilmin shugabanci na tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel, dake Abekuta, Daily Trust ta ruwaito.
"Muna da yan sanda 400,000 a Najeriya, amma 200,000 na tare da yan siyasa. Abinda muke a kasar nan kawai yan siyasa ake tsaro, ba ma tsaron jama'a, kuma abinda ya kamata mu duba ne," Arase yace.
Arase ya ce ummul haba'isin matsalolin da ake samu a hukumar yan sandan Najeriya rashin son gyaran yan siyasa ne.
Yace tun shekarar 1999, Najeriya ta yi kwamitocin gyara hukumar har guda hudu "amma kaico, babu gyaran da akayi amfani a shi. Takardun na nan an ajiyesu suna rufe da kura."
KU KARANTA: Gara a rasa mulki amma a tsira da mutunci - Jonathan
Wannan ya biyo bayan umurnin da Sifeton yan sanda ya baiwa manyan jami'ansa a karshen makon da ya gabata.
Sifeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya bada umurnin janye dogaran dake wajen attajirin dan kasuwa, Emeka Offor; Fani-Kayode, manyan malamai da kamfanoni da fadin tarayya.
Wannan umurni ya shafi mutane 60, kamfanoni, cocuna da kungiyoyin addini.
KU KARANTA: Babu abinda dakatad da Rahama Sadau zai canza a masana'antar Kannywood - Farida Jalal
Daga ciki akwai Christ Embassy, Think Nigeria First Initiative, Uche Sylva International, Stanel Groups, da KYC Holding
Sauran sune Sen Lado Yakubu, Amb. Yuguda Bashir, Uche Chukwu, Sen. Boroface Ajayi, Mutiu Nicholas, Sen. Tokunbo Afikuyomi, Edozie Madu, David Adesanya, Chris Giwa, Chief Godwin Ekpo, Chief Pius Akinyelure da sauransu.
Hakan na kunshe cikin wasika mai lamba .CB: 4001/IGP.SEC/ABJ/VOL.116/32 da rana wata 4 ga Nuwamba, da IGP ya aikewa dukkan kwamishanonin yan sandan jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng