Mutane Sun Tsere daga Gidajensu a Benue da 'Yan Bindiga Suka Kai Mugun Hari

Mutane Sun Tsere daga Gidajensu a Benue da 'Yan Bindiga Suka Kai Mugun Hari

  • Al'ummar garin Otobi da ke jihar Benue sun shiga tashin hankali yayin da ‘yan bindiga suka kai masu hari da yammacin ranar Talata
  • Yayin da ake fargabar an samu asarar rayuka, rahoto ya nuna cewa mazauna Otobi sun far tserewa suna barin gidajensu saboda firgici
  • Dan majalisar Benue, Kennedy Angbo, da ciyaman na Otukpo, Maxwell Ogiri, sun tabbatar da harin tare da neman a dauki matakin gaggawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Fargaba ta mamaye al’ummar Otobi da ke yankin Akpa a karamar hukumar Otukpo, jihar Benue, bayan wani sabon hari da ‘yan bindiga suka kai.

Wasu mazauna yankin sun shaida wa manema labarai ta wayar salula cewa ana fargabar wasu sun mutu a harin da aka kai da misalin karfe 6:30 na yamma.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan farmaki wurin ibada, sun yi awon gaba da mutane

'Yan bindiga sun farmaki jihar Benue
Jihar Benue: "Yan bindiga sun tilasta mutane barin gidajensu. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

'Yan bindiga sun farmaki jihar Benue

Rahoton Punch ya nuna cewa maharan sun kai harin ne a ba-zata, lamarin da ya sa mutane guduwa daga gidajensu domin tsira da rayukansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kennedy Angbo, dan majalisar Benue da ke wakiltar mazabar Otukpo-Akpa, ya tabbatar da kai harin ga manema labarai ta wayar salula daga Makurdi.

Ya bayyana cewa har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda harin ya rutsa da su ba, amma jama’a da dama sun tsere daga gidajensu.

Mazauna Benue sun fara gudun ceton rai

Wani mazaunin yankin, Edwin Emma, wanda ya tsallake rijiya da baya, ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kai harin a lokacin da mutane ke harkokin gabansu.

Edwin Emma ya ce:

“Makiyaya ne suka kai mana hari a Otobi. Yanzu haka da nake magana da ku, matata da ‘ya’yana na can suna gudun neman mafaka. A taimake mu don Allah.”

Edwin ya bukaci gwamnatin jihar da hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa, yana mai cewa an kai masu harin ba tare da wani dalili ba.

Kara karanta wannan

Yaki da yunwa: An ba malaman gona babura 300 domin shiga lungu da sako a Jigawa

Rahoto ya nuna cewa a garin Otobi ne aka gina babbar madatsar ruwa ta ma’aikatar ruwa ta tarayya, inda aka taba kai masu hari a cikin watan nan.

A lokacin harin da aka kai a baya, rahotanni sun nuna cewa an kashe wani mai gadi da ke kula da madatsar ruwan, inji rahoton Vanguard.

Ciyaman ya fadi abin da ya faru

Shugaban karamar hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya tabbatar da harin ga manema labarai ta wayar salula, yana mai cewa ya tuntubi jami'an tsaro.

A cewar Maxwell:

“Ina Abuja domin sauraron hukuncin kotun zaben kananan hukumomi, lokacin da aka kira ni, aka sanar da ni cewa Otobi na fuskantar mummunan hari.”

Maxwell Ogiri ya bayyana cewa ya umarci hadimansa da ke Otobi da kewaye su hada kai da jami’an tsaro domin shawo kan lamarin.

Ya kara da cewa har yanzu bai samu cikakken rahoto ba, amma bayanai na farko sun nuna cewa Fulani makiyaya ne ake zargi da kai harin.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun sake tabargaza a Filato, sun kashe mutane kusan 50

“A halin yanzu, ban samu rahoton ko an kashe wani daga hukumomi ba, amma ina sa ran samun karin bayani nan gaba,” inji shugaban.

Ba a ji ta bakin 'yan sanda ba

Ba a ji ta bakin rundunar 'yan sanda kan wannan hari da aka kai Filato ba
Shugaban 'yan sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Maxwell Ogiri ya bukaci al’umma su kwantar da hankalinsu tare da barin jami’an tsaro su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Duk kokarin da aka yi don jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Benue ya ci tura, domin ba a amsa kiran waya da sakonni ba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, CSP Catherine Anene, ba ta mayar da amsa ga kira da sakonnin da aka aike mata ba har zuwa lokacin hada rahoton.

Mutane 54 aka kashe a harin Filato

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa, Amnesty International ta ce mutane 54 ne 'yan ta'adda suka kashe a Filato.

Rahoton Amnesty International ya nuna cewa 'yan ta'addar sun farmaki mutane cikin ba-zata, lamarin da ya jawo asarar rayuka da dama, yayin da ake neman wasu mutanen.

Sakamakon kisan gomman mutanen, shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci gwamnan Filato, Caleb Mutfwang da ya gaggauta kawo karshen zubar da jinin da ake yi a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng