Tirƙashi: Saudiyya na Barazanar Ɗaure Alhazan Najeriya da Wasu Ƙasashe kan Umrah

Tirƙashi: Saudiyya na Barazanar Ɗaure Alhazan Najeriya da Wasu Ƙasashe kan Umrah

  • Gwamnatin Saudiyya ta ce duk maniyyacin da bai bar ƙasar kafin 29 ga Afrilu 2025 ba, zai fuskanci hukunci kamar dauri ko tarar kudi
  • Saudiyya na amfani da AI wajen duba cunkoso, don haka wanda ya karya dokar biza yana zama barazana ga tsarin gudanar da aikin Hajji
  • 'Yan Najeriya da sauran kasashen da ke zuwa Umrah, za su fuskanci daurin watanni ko/da tarar da ta haura riyal 45,000 idan suka karya doka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Saudiyya - Gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa za ta fara daure duk wani maniyyacin Umrah da ya keta sharuddan biza ko ya ƙi barin ƙasar kafin 29 ga Afrilu.

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta tabbatar da cewa 29 ga Afrilu 2025 ita ce ranar ƙarshe da dukkanin maniyyatan Umrah ya kamata su bar Saudiyya.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon ɗan wasa kuma Kocin Super Eagles ya rasu a shekara 74

Saudiyya ta gargadi masu zuwa Umrah amma su ki komawa gida bayan karewar bizarsu
Alhazai na gudanar da dawafi a Ka'abah, kasar Saudiyya. Hoto: @insharifain
Asali: Facebook

Saudiyya ta gargadi maniyyatan Umrah

Wanda ya ci gaba da zama bayan wannan rana zai fuskanci tara mai tsanani, ɗauri a kurkuku, da sauran nau'ukan hukunci, inji rahoton Gulf News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mataki na cikin shirin Saudiyya na fara shirye-shiryen aikin Hajjin bana, tare da nuna damuwa kan yadda wasu baƙi ke ƙoƙarin fakewa su ci gaba da zama bayan izinin Umrah.

Shugaban sandan Saudiyya, Laftanar Janar Mohammed Abdullah Al Bassami ya ce:

“Muna da tsari na kare mutunci da amincin baƙin Allah da tabbatar da ingancin shirin sarrafa cunkoso tare da hukumomin tsaro, soja da na farar hula, ba za mu lamunci wata matsala ba."

Yadda Saudiyya ke amfani da fasahar AI

Hukumomin Saudiyya sun jaddada muhimmancin kiyaye doka da oda da kuma mutunta tsarin aikin Hajji da Umrah.

Wuce kwanakin izini ko ƙoƙarin kauce wa dokokin biza na kawo cikas ga tsare-tsaren tsaro da na dabarun kula da al’umma, musamman yadda Saudiyya ke dogaro da fasahar kere-kere da na’urar AI wajen tafiyar da miliyoyin maniyyata.

Kara karanta wannan

Kisan Hausawa a Edo: Majalisa na neman sauya fasalin aikin 'yan banga

An rahoto cewa yanzu Saudiyya na amfani da fasahar AI wajen duba cunkoso da daidaita yawan jama’a tun daga shigowa birnin Makkah har zuwa Masallacin Harami.

An ce wadannan fasahohin na zamani na ba da damar saurin shawo kan cunkoso da tabbatar da tsaro yayin Umrah da aikin Hajji.

Illar da keta dokar biza ke yi wa Saudiyya

Hukumomi sun ce yawan maniyyata fiye da ƙima ko ƙin barin ƙasar idan an kammala Umrah na iya kawo tarnaki ga tsarin da ke tafiyar da aikin Hajji.

Laftanar Janar Adel Zamzami (mai ritaya), kwararren masanin tsaro, ya ce Saudiyya na sahun gaba wajen amfani da fasahar birane na zamani wajen gudanar da Hajji.

“Dukkan shirye-shirye na mayar da hankali ne kan ɗan adam – wato maniyyaci. Idan mutum ya karya doka, yana barazana ga tsarin da aka gina shi kan haɗin kai da inganci,” inji Adel.

Ma’aikatar cikin gida ta Saudiyya ta riga ta kaddamar da tawagar haɗin gwiwa da za ta rika kai samame a fadin ƙasar domin kama masu karya dokokin zaman ƙasa.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: An so rufe Sanusi II a Abuja, a saka dokar ta baci a Kano

Hukuncin da za a yanke wa maniyyata Umrah

An ji hukuncin da za a yanke wa maniyyatan Umrah da suka ki komawa gida bayan karewar bizarsu
Dubunnan daruruwan alhazai yayin da suke gudanar da aikin Hajji a Saudiyya. Hoto: @insharifain
Asali: Facebook

Daga 27 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, hukumomi sun kama fiye da mutane 18,400 saboda karya dokokin zama, aiki da kuma tsallake iyaka.

Cikin waɗanda aka kama, 12,995 sun karya dokar zama ne, yayin da sama da 3,500 aka kama suna ƙoƙarin keta iyaka ba bisa ƙa’ida ba.

Ahmad Al Maliki, wani babban lauya a kasar, ya ce wanda ya fara karya dokar biza zai fuskanci tarar riyal 15,000 (kimanin $4,000).

Idan ya maimaita wannan laifin, za a iya cin shi tara har ta riyal 25,000, da daurin watanni uku da kuma korar mutum daga ƙasar.

Idan ya ci gaba da maimaita laifin, zai fuskanci tara har ta riyal 50,000, watanni shida a gidan yari da kuma takardar tuhuma.

Saudiyya ta hana 'yan Najeriya bizar Hajji?

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumomin Saudiyya sun karyata rahotannin da ke cewa wasu ƙasashe 13 ciki har da Najeriya, Jordan, Sudan da Iraq an hana su samun biza.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dauki babban mataki da Amura ta kakaba haraji kan Najeriya

Rahoton ya yi ikirarin cewa dokar hana bizar za ta fara aiki daga 13 ga Afrilu, kuma masu karya ta za su fuskanci haramcin shiga Saudiyya na wasu shekaru.

Sai dai Cibiyar Yawon Buɗe Ido ta Saudiyya ta bayyana cewa babu batun hana biza, amma an ɗan takaita zirga-zirgar masu yawon buɗe ido zuwa Makka a lokacin Hajji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng