'Ka Tsaya Matsayinka': Gargadin da Shettima Ya Yi wa Shugaban Hukumar Alhazai
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya gargadi Farfesa Abdullahi Saleh-Usman, kan gudanar da hukumar NAHCON shi kaɗai
- Shettima ya bayyana cewa dokar da ta kafa NAHCON ba ta bai wa mutum guda ikon gudanar da hukumar ba tare da kwamishinoni ba
- Gargadin ya zo bayan korafe-korafen da kwamishinoni takwas suka shigar, inda suka zargi shugabansu da rashin adalci da karya ka’idoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya aika sakon gargadi mai karfi ga shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh-Usman.
Shettima ya gargadi Farfesa Abdullahi da ya kiyayi kansa da yin babakere a wajen gudanar da hukumar NAHCON, kamar tashi ce shi kadai.

Asali: Twitter
Shettima ya yi wa shugaban NAHCON gargadi
Gargadin ya fito ne a cikin wata wasika da ofishin mataimakin shugaban ƙasar ya aikewa shugaban hukumar alhazan, dangane da wasu zarge-zarge, inji rahoton Daily Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce gargadin ya biyo bayan wasu zarge-zarge da ake yi wa Farfesa Abdullahi da suka shafi sayen kayayyaki, da nada hadimai ba bisa ka'ida ba.
Sauran zarge-zargen sun hada da rashin iya kyakykyawan jagoranci, watsi da 'yan kwamitin gudanarwar hukumar da dai sauransu.
"NAHCON ba ta mutum 1 ba ce': - Shettima
Wasikar, mai ɗauke da kwanan wata 17 ga Maris, na ɗauke da sa hannun mataimakin shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia.
Shettima ya nuna rashin jin daɗinsa da yadda shugaban NAHCON ke ware kwamishinonin hukumar a muhimman ayyuka, wanda hakan ya saɓa wa dokar da ta kafa hukumar.
A cewarsa:
“Dokar da ta kafa NAHCON ba ta bai wa wani mutum damar tafiyar da hukumar shi kaɗai ba. Kowanne memba yana wakiltar yankin da ya fito ne, musamman a harkokin jin daɗin alhazai.”
Shettima ya ja kunnen shugaban NAHCON

Asali: Twitter
Ya ƙara da cewa an sha gabatar da ƙorafe-ƙorafe, ciki har da taron ranar 4 ga Fabrairu 2025, inda shugaban NAHCON ya amsa kura-kuran kuma ya bada hakuri, amma bai ɗauki matakin gyara ba.
SaharaReporters ta rahoto wasikar ta kara da cewa:
“Mai girma mataimakin shugaban kasa ya ba da umurnin a ja hankalinka game da tanadin dokar NAHCON, wacce ke bayani a fili cewa ikon yanke hukunci da gudanarwa ya rataya ne a kan hukumar gaba ɗaya, ba a kan mutum guda ba.”
Shettima ya ja kunnen Farfesa Usman da cewa wajibi ne ya tabbatar membobin hukumar sun sami damar aiwatar da ayyukansu kamar yadda dokar hukumar ta tanada.
Kwamishinonin NAHCON sun kai karar Saleh-Usman
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan kwamitin gudanarwar hukumar NAHCON sun kai ƙarar Farfesa Abdullahi Saleh-Usman zuwa ofishin mataimakin shugaban ƙasa.
Kwamishinoni takwas da ke wakiltar yankunan kasa da kungiyoyin addini, NSCIA, JNI, sun zargi shugaban NAHCON da kauce wa tsarin gudanar da hukumar.
Sun shaidawa Kashim Shettima cewa yanzu Farfesa Saleh-Usman ya ware su daga kusan dukkanin harkokin gudanarwar hukumar, sai dai suka ga ana yi daga nesa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng