Rigimar NAHCON Ta Ƙi Ƙarewa, Shettima ya Kira Sheikh Pakistan taron gaggawa a Abuja
- Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kira shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan da mambobin kwamitin gudanarwa taro a Abuja
- Akwai rikici tsakanin shugaban NAHCON da wasu mambobin kwamitin da suka kai ƙorafi kan rashin aiki da su, shugaban ya na yin gaban kansa a hukumar
- Mataimakin Shugaban Ƙasa a baya ya ja kunnen shugaban NAHCON kada ya cigaba da tafiyar da hukumar tamkar shugaba ɗaya ba tare da jansu ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya gayyaci Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan.
Kashim Shettima ya yi kiran ne ga shugaban NAHCON da mambobin kwamitinsa zuwa wani taro yau Talata 22 ga watan Afrilun 2025.

Asali: Facebook
Wannan na cikin wata wasiƙa da Daily Trust ta gani, mai ɗauke da sa hannun Sanata Ibrahim Hassan Hadejia daga ofishin mataimakin shugaban ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NAHCON: Kashim Shettima ya gargadi Sheikh Pakistan
Wannan ya biyo bayan wata sanarwa da ake yaɗawa cewa Kashim Shettima ya gargadi shugaban NAHCON kan salon shugabancinsa.
An ce mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya gargadi Farfesa Abdullahi Saleh-Usman Pakistan kan gudanar da hukumar NAHCON shi kaɗai.
Shettima ya bayyana cewa dokar da ta kafa NAHCON ba ta bai wa mutum guda ikon gudanar da hukumar ba tare da kwamishinoni ba.
Gargadin ya zo bayan korafe-korafen da kwamishinoni takwas suka shigar, inda suka zargi shugabansu da rashin adalci da karya ka’idoji.
Matsalar da ke tsakanin Pakistan da mambobinsa
Ana iya tunawa cewa shugaban NAHCON da wasu mambobin hukumar sun samu sabani kan yanke shawarar da shugaban ke yi ba tare da tuntubarsu ba.
Wannan ya kai ga mambobin kwamitin yin ƙorafi ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, wanda ya gargadi shugaban NAHCON da ya daina mulki da kansa kawai.
Sai dai shugaban hukumar ya musanta zargin da aka yi masa na cewa yana gudanar da hukumar shi kaɗai ba tare da shawarwari da sauran mambobi ba.

Asali: Twitter
Kashim Shettima ya kira taron gaggawa a NAHCON
Sanarwar ta ce za a gudanar da taron a yau Talata 22 ga watan Afrilun 2025 da misalin karfe 1:30 na rana a Abuja.
A cewar wasiƙar:
“An umurce ku, ku halarci taro da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima GCON, a ranar Talata 22 Afrilu 2025, da misalin 1:30 na rana.
“Da fatan za ku sanar da sauran mambobin kwamitin ku zo da takaitaccen rahoto kan shirye-shiryen aikin hajjin 2025 da batutuwan da ba a warware ba."
Sheikh Pakistan ya hango matsala a aikin hajji
Kun ji cewa shugaban hukumar kula da maniyyatan Najeriya watau NAHCON, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan ya ce da yiwuwar a fuskanci zafin rana a hajjin bana.
Sheikh Pakistan ya gargaɗi masu shirin sauke farali a 2025 su shirya fuskantar zafin rana mai tsanani yayin da hukumar ta ke nata shirye-shiryen.
Ministam lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya ziyarci NAHCON a Saudi domin duba matakai da kayayyakin da aka tanada don kula da lafiyar maniyyata.
Asali: Legit.ng