Gwamnati Ta Fadi Laifin da zai Jawo Daurin Shekaru 10 ga Masu Amfani da Intanet

Gwamnati Ta Fadi Laifin da zai Jawo Daurin Shekaru 10 ga Masu Amfani da Intanet

  • Hukumar kula da hannayen jari ta ƙasa ta fitar da gargaɗi ga a masu amfani da kafafen sada zumunta kan tallata shafukan talla da ba su da rajista
  • Rahotanni sun nuna cewa dokar hannayen jari ta 2025 ta ba SEC damar kamawa da gurfanar da duk masu tallata irin wadannan shafuka
  • SEC ta bayyana cewa tana aiki tare da EFCC da ‘yan sanda domin cafke masu damfara, musamman bayan rushewar dandalin CBEX

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar kula da hannayen jari ta ƙasa (SEC) ta yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta da su guji tallata kamfanoni marasa rajista.

SEC ta fadi haka ne tana mai cewa sabuwar dokar da aka amince da ita a shekarar 2025 ta ba da damar hukunta irin wadannan laifuffukan.

Dr Agama
Za a fara daure masu tallata hajojin bogi a intanet. Hoto: @SECNigeria
Asali: Twitter

The Guardian ta wallafa cewa shugaban hukumar, Dr Emomotimi Agama ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da manema labarai a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr Emomotimi Agama ya ce dole ne a ɗauki matakan kare al’umma daga masu damfarar jama’a da sunan zuba hannun jari.

Hukuncin masu tallata shafukan bogi

A cewar shugaban hukumar, sabuwar dokar ISA 2025 ta ƙara wa hukumar ƙarfi wajen hukunta wadanda ke tallata shafukan bogi, musamman a dandalin sada zumunta.

Punch ta wallafa cewa Dr Agama ya ce:

“Sabuwar dokar ta tanadi hukunci mai tsanani ga duk masu tallata shafukan zuba hannun jari marasa rajista, ciki har da ɗaurin shekaru 10 da kuma tarar Naira miliyan 20.”

Ya jaddada cewa SEC na aiki da EFCC, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin bankadowa, kamawa da gurfanar da duk wadanda ke da hannu a irin wadannan laifuffuka.

Agama ya ce tallata shafukan da ba su da rajista babban laifi ne, don haka ya gargadi duk masu amfani da a kafafen sada zumunta da su daina wannan aiki ko su fuskanci fushin doka.

Sanda
Za a hada kai da 'yan sanda don kama masu tallata shafukan bogi a intanet. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Matakan da aka dauka bayan rushewar CBEX

A cikin makonnin baya-bayan nan, rushewar wani dandalin zuba jari mai suna CBEX ya jefa dubban mutane cikin asara bayan an ce ya damfari al’umma har N1.3tn.

SEC ta bayyana cewa wannan lamari ya zama darasi ga masu zuba jari da ke bin shafuka marasa tushe.

Dr Agama ya ce:

“Za mu rufe ayyukansu, kuma wadanda ke da hannu za su fuskanci hukunci,”.

Agama ya bayyana cewa hukumar ta ƙaddamar da shirye-shiryen fadakar da jama’a ta hanyoyi da dama domin kare dukiyarsu.

Hukumat EFCC ta yi wa 'yan Najeriya wa'azi

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC ta dauki sabon salon yi wa mutane wa'azi da ayoyin Kur'ani da Bible.

Hukumar tana kira ga al'umma da su guji cin dukiyar kasa ko ta mutane ba bisa ka'ida ba domin kaucewa fushin doka.

Legit ta rahoto cewa hukumar ta ce ko da mutane ba su gamsu da dokar EFCC ta hana satar kudi ba, to su sani cewa Allah ya hana yin hakan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng