Sarkin Musulmi, Obasanjo Sun Hada Kai a Aikin Allah, Sun Bukaci Taimako a Gyaran Masallaci
- Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya bukaci 'yan Najeriya su rika yin ayyukan alheri domin samun lada daga Allah
- Dattijon wanda ya yi shekaru kimanin 10 a mulkin Najeriya ya yi kiran ne yayin kaddamar da gyaran masallaci a garin Egba
- An bayyana sabon fasalin masallacin da ke Abeokuta, wanda zai kunshi sashen karatu, asibiti, ofisoshi, da wuraren zamantakewa
- Sarkin Musulmi da sauran manyan baki sun yaba da aikin, inda aka ce gidaje 78 za a rushe kuma a samar da sabbin matsuguni
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ogun - Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya bukaci 'yan Najeriya su rungumi taimako, yana mai cewa irin wadannan ayyuka na janyo lada.
Obasanjo ya roki hadin kai da kuma bayar da tallafi domin gyaran babban masallacin Juma'a da ke Egba a jihar Ogun.

Asali: Facebook
Obasanjo ya shawarci yan Najeriya kan taimako
A cewar wata sanarwa, Obasanjo ya bayyana haka ne yayin kaddamar da sabon tsarin ginin babban masallacin Egba da ke Abeokuta, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da bikin bude wannan tsari ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Shirin, wanda Majalisar Musulman Egba ta tsara, ya hada da gyaran masallacin da kara wasu gine-gine da suka hada da ofisoshi da makarantun addini.
Obasanjo ya bukaci dukkan 'yan Najeriya su mara wa aikin baya, yana mai cewa irin wannan taimako yana da lada a wajen Ubangiji.
Ya ce:
“Wannan aiki ne da kowa zai iya bayar da gudunmawa, don a kammala shi cikin gaggawa da hadin gwiwar kowa da kowa.”
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, wanda mataimakiyarsa ta wakilta, ya bayyana aikin a matsayin ci gaba ga Musulman Egba da al'ummar jihar.
Ya yaba da rawar da Obasanjo ke takawa wajen karfafa hadin kai da zaman lafiya, ya kuma bukaci jama’a su kasance masu hakuri da juna, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Twitter
Sarkin Musulmi ya yabawa Musulman Egba
Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ya yaba da kokarin Majalisar Musulman Egba tare da yiwa ‘yan Najeriya kira su ci gaba da bayar da gudunmawa.
Ya ce zai tuntubi wasu manyan mutane domin hada karfi da karfe wajen ganin an kammala aikin sabon masallacin cikin lokaci.
Sarkin kasar Egba, Oba Adedotun Gbadebo, ya bayyana muhimmancin aikin ga tarihi da ci gaban al’adun Musulunci da na gargajiya a yankin.
Sheikh Sulaimon-Faruq Onikijipa ya ce masallatai na da muhimmanci a Musulunci, inda suka zama cibiyoyin zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Ya bukaci jama’a su bayar da gudunmawa domin samun lada daga Allah tare da tallafa wa aikin masallacin a duk inda suke.
Obasanjo ya gano matsalar talauci a Najeriya
Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan talaucin da ya addabi ƴan Najeriya.
Obasanjo ya bayyana cewa bai kamata ƴan Najeriya su kasance cikin talauci ba duba da irin ɗumbin albarkatun da ƙasar ke da su.
Tsohon shugaban ya nuna cewa matsalar talaucin da ake fama da ita ta ta'allaƙa ne da yadda ake tafiyar da albarkatun ƙasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng