Filato: Ƴan sanda Sun Motsa, Asirin Manya 2 da Ake Zargi da Kisan Rayuka 50 Ya Tonu
- Rundunar ƴan sanda ta ɗauki tsauraran matakai domin magance hare-haren ta'addanci a jihar Filato da ke Arewacin Najeriya
- Mai magana da yawun rundunar ya tabbatar da kama manyan waɗanda ake zargi da hannu a hare-haren da suka jawo asarar rayuka sama da 50
- Sufetan Ƴan Sanda na Ƙasa, IGP Kayode Egbetokun ya kai ziyara Filato, kuma ya ba da umarnin tura dakaru na musamman don kare rayuka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau - Sufeto Janar na Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun, ya sake nuna damuwarsa kan hare-haren kisan gilla da ke ci gaba da faruwa a Jihar Filato.
IGP Kayode Egbetokun ya bayyana kashe-kashen Filato a matsayin “munana kwarai, kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa.”

Asali: Twitter
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa Rundunar ‘Yan Sanda ta ƙasa ta wallafa a shafin X ɗauke da sa hannun mai magana da yawunta, ACP Olumuyiwa Adejobi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sufeto Janar ya bayyana alhini da bakin ciki bisa asarar rayuka da aka yi, lokacin da ya kai ziyara jihar Filato a ranar Talata, 15 ga watan Afrilu, 2025.
Ƴan sanda sun cafke mutum 2 a Filato
Sanarwar ta bayyana cewa an kama manyan mutane biyu da ake zargi da hannu a harin da aka kai a Karamar Hukumar Bokkos, kuma tuni bincike ya yi nisa domin gano duka masu hannu.
Ta ce waɗanda aka kama sun fara ba da haɗin kai ta hanyar bayar da bayanan da za su taimakawa dakarun ƴan sanda wajen kamo masu hannu a lamarin.
“Rundunar ‘Yan Sanda ta na ci gaba da bincike don gano dalilan da suka haifar da wadannan hare-hare tare da kama sauran wadanda suke da hannu a ciki,” in ji Adejobi.
Wane mataki rundunar ƴan sanda ta ɗauka?
Ya ce Sufeto Janar ya umarci mataimakinsa (DIG) mai kula da harkokin ayyuka, Kwazhi Dali Yakubu, da ya jagoranci dukkan ayyukan ‘yan sanda a Jihar Filato.
A cewarsa, tun bayan haka ne DIG ya fara sintiri da jirgin sama a yankunan Bokkos da Bassa, tare da ganawa da shugabannin al'umma domin karfafa wa jama'a gwiwa.
"Bayan nazari kan matakan tsaro da aka dauka, IGP ya bada umarnin tura karin jami’an tsaro da kayan aiki zuwa jihar domin dakile hare-hare da kara tsaurara tsaro," in ji shi.
Rundunar ƴan sanda ta kuma fara tantance yankuna masu hadari domin tura jami’ai yadda ya kamata, su ba al'umma kariya.

Asali: Facebook
Sufetan ƴan sanda ya jajantawa mutanen Filato
IGP ya tabbatar wa al’ummar Filato cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa don dawo da zaman lafiya, tare da kira ga jama’a da su zauna lafiya, su bayar da hadin kai da bayanai masu amfani.
Ya kuma jajantawa iyalan wadanda aka rasa a hare-haren tare da bayyana goyon bayansa da jaje ga daukacin al’ummar jihar a wannan lokaci mai wahala.
Rundunar ƴan sanda ta kuma yi alkawarin kamo duk masu hannu a harin domin fuskantar fushin doka, tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Gwamnan Filato ya ba jama'a haƙuri
A baya, kun ji cewa gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya bai wa mutane haƙuri bisa kisan rayukan da aka yi kwanan nan a wasu garuruwa a jihar.
Gwamna Mutfwang ya nemi afuwar ne daga wajen al’ummar ƙaramar hukumar Bassa kan gazawar gwamnati da hukumomin wajen tabbatar da tsaron jama'a.
Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 51 ne suka rasa rayukansu a munanan hare-haren da aka kai garin Zikke da ke yankin karamar hukumar Bassa a Filato.
Asali: Legit.ng