Tura Ta kai Bango: Gwamnan Edo Ya Fadi Hukuncin da Zai Yi Wa Masu Garkuwa da Mutane

Tura Ta kai Bango: Gwamnan Edo Ya Fadi Hukuncin da Zai Yi Wa Masu Garkuwa da Mutane

  • Gwamnan Edo, Sanata Monday Okpebholo ya bayyana cewa za a riƙa aiwatar da hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane a jihar
  • Monday Okpebholo ya nuna cewa zai sanya hannu domin aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da aikata laifin
  • Okpebholo ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da aikata miyagu ayyuka a jihar ba domin ya shirye kare rayukan mutane da dukiyoyinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Gwamnan Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya bayyana shirinsa kan masu garkuwa da mutane a jihar.

Gwamna Monday Okpebholo ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane da aka kama a jihar za a yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Gwamna Monday Okpebholo
Gwamna Okpebholo zai zartar da hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane Hoto: @m_akpakomiza
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Fred Itua, ya fitar a ranar Juma’a, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a kashe masu garkuwa da mutane a Edo

Gwamna Okpebholo ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a zauren taro na Uromi, inda ya tattauna da shugabanni da mambobin al’ummar Arewa da ke ƙasar Esan.

Ya bayyana cewa majalisar dokokin jihar Edo ta amince da wata doka da ta gyara dokar haramta garkuwa da mutane (da sauran dokoki masu alaƙa da ita na shekarar 2013).

Ya ce wannan sabuwar doka ta tanadi hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane tare da umarnin ƙwacewa da rusa dukiyoyin da aka yi amfani da su wajen aikata laifin.

Gwamnan ya nuna cewa zai sanya hannu a kan takardar hukuncin kisan duk wani garkuwa da mutane da aka kawo masa.

Gwamnan jihar Edo bai wasa da rashin tsaro

Gwamna Okpebholo ya ce gwamnatinsa ba za ta yarda da rashin tsaro, kisa, da garkuwa da mutane a jihar ba, kuma zai ɗauki matakin gallazawa duk wani mai aikata laifi.

Monday Okpebholo
Gwamna Okpebholo ya bukaci a hada kai kan matsalar rashin tsaro Hoto: @m_akpakomiza
Asali: Twitter
“Ina ɗaukar batun rashin tsaro da muhimmanci matuƙa, kuma ba zan keta doka ba, sai dai na aiwatar da ita yadda ya kamata."
"Sabuwar dokar da muka yi a jihar ta ba mu damar rusa dukiyoyinsu da kwace filayensu. Za mu gina ofisoshin ƙungiyoyin sa-kai a kan waɗannan filaye."
Za mu fito da masu garkuwa da mutane a bainar jama’a mu aiwatar da hukuncin kisa a kansu don nuna mu da gaske muke, kamar yadda dokar majalisar dokoki ta tanada. Ba zan ji tsoron sa hannu ba."

- Gwamna Monday Okpebholo

Gwamnan ya buƙaci jama'a da su haɗa kai da gwamnatinsa domin tabbatar da tsaro a jihar, inda ya nuna cewa tsaro aiki ne na kowa, ba na jami’an tsaro kaɗai ba.

Gwamna ya fara yaƙin neman zaɓen Tinubu a Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya ƙaddamar da yaƙin neman sake zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Monday Okpebholo ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ne a jihar Edo, inda ya nuna cewa sun shirya goyon bayan shugaban ƙasan.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa mutane da dama na shirin shigowa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Edo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng